1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi sababbin ministoci a gwamnatin Tarayyar Jamus

December 16, 2013

Bayan da jam'iyyu suka kammala zaben ministoci, majalisar dokoki ta Bundestag zata yi zaman taro ranar Talata inda za'a nada sabuwar gwamnatin Jamus ta hadin gwiwa

https://p.dw.com/p/1AagR
Hoto: Reuters

Watanni ukku bayan zaben majalisar dokoki a nan Jamus, an kammala dukkanin shirye-shirye na kafa sabuwar gwamnatin taraiya ta hadin gwiwa tsakanin jam'iyar CDU ta shugaban gwamnati, Angela Merkel da kawarta CSU da kuma jam'iyar Social Democrats wato SPD. Bayan da 'ya'yan jam'iyar SPD a wata kuri'a ta jin ra'ayi suka amince da yarjejeniyar kafa gwamnatin, jam'iyun gaba daya sun sanar da jerin ministocinsu, kuma ana sa ran gobe Talata za'a gabatar da Angela Merkel a majalisar dokokin domin a zabe ta karo na uku kan mukamin na shugaban gwamnati.

Tun a ranar Litinin shugaban kasa, Joachim Gauck ya gabatar da sunan Angel Merkel, shugaban gwamnati ta rikon kwarya tun bayn zaben da aka yi a watan Satumba, domin majalisar dokoki ta zabe ta a matsayin shugaban gwamnati. Tun da farko sai da jam'iyun na CDU da CSU da kuma SPD suka sanya hannu kan yarjejeniyar kafa gamnatin ta hadin giwa da zata yi mulki daga yanzu zuwa wasu shekaru hudu masu zuwa. Karkashin wannan yarjejeiya, jam'iyar CDU zata kasance da mukaman ministoci biyar da shugaban gwamnati da kuma minista daya a ofishin shugaban gwamnati. Jam'iyar CSU mai kawance da ita, zata bayar da mukaman ministoci uku, yayin da jam'iyar SPD zata kasance da mukamai na ministoci shidda.

A bayan sanya hannu kan yarjejeniyar ta gwamnatin hadin gwiwa a Berlin, shugaban gwamnati Angela Merkl ta baiyana burin gwamnatin da zata kama mulki nan gaba kadan.

Tace bukatarmu ita ce mu ga al'ummar Jamus, sun sami ci gaba, rayuarsu ta kyautata daga nan zuwa shekara ta 2017, fiye da yadda al'amarin yake a yanzu.

Sabon ministan harkokin waje a gwamnatin ta hadin gwiwa, shine Frank-Walter Steinmeier dan jam'iyar SPD, wanda ba bako bane a wannan ma'aikata. Ya taba rike wannan mukami a gwamnatin hadin gwiwa ta manyan jam'iyun CDU da CSU da SPD da tayi mulki tsakanin shekara ta 2005 zuwa 2009. Ministan kudi, Wolfgang Schäuble shima dai ba bako bane a wannan ma'aikata, saboda yanzu ma shine kan wannan mukami. Shugaban jam'iyar SPD, Sigmar Gabriel, ya karbi gagarumin nauyi a kansa na kula da ma'aikatar tattalin arziki da makamashi. Daga cikin nauyin dake kansa, har da neman ika burin gyara batun makamashi da sabunta tsarin samar da makamashi a nan Jamus. Mukamin da yafi daukar hankali, kuma yafi zama na ba-zata shine nada tsohuwar ministan iyali, Ursula von der Leyen yar jam'iyar CDU a matsayin sabuwar ministan tsaro. Wannan dai shine karon farko a tarihin Jamus da aka baiwa mace wannan mukami na shugabancin rundunar tsaron Jamus. A kan wannan mukami, von der Leyen ta gaji Thomas de Meiziere, wanda aka nada sabon ministan cikin gida. Dangane da jerin ministocin da majalisar ministocin ta Jamus ta kunsa da kuma yarjejejiiyar da ya snya hannu tare da CDU, shugaban jam'iyar SPD, Sigmar Gabriel ya nunar da cewar:

Ursula von der Leyen
Sabuwar ministan tsaron Jamus, Ursula von der LeyenHoto: picture-alliance/dpa

A ra'ayi na, wannan yarjejeniya ce da ta nunr da ta manyan jam'iyu da aka cimma musamman domin masu karamin karfi su ci gajiyarta.

Sabuwar minista a ma'aikatar iyali, mata da matasa ita ce Manuela Schwesig daga jam'iyar SPD, yayin da sabon ministan taimakon raya kasashen ktetare shine dan jam'iyar CSU Gerd Müller, sa'annan da minista Johanna Wanka zata ci gaba da rike ma'aikatar ilimi mai zurfi.

Sigmar Gabriel Minister für Wirtschaft und Energie
Shugaban jam'iyyar SPD Sigmar Gabriel, ministan tattalin arziki da makamashiHoto: picture-alliance/dpa

Idan majalisar dokoki ta Bundestag ta hallara domin zaman taron ta ranar Talata, wakilai zasu amsa shawarar da shugaban kasa ya bayar game da zaben Angela Merkel kan mukamin shugaban gwamnati. Wannan mataki kuwa ba zai zama da tantama ba, saboda gagarumin rinjayen da jam'iyun na hadin gwiwa, wato CDU da CSU da SPD suke dashi a majalisar ta Bundestag. Bayan rantsar da ita a majalisar, shugaban kasa Gauck zai rantsar da sabbin ministocin da zasu taimaka wajen tafiyar da gwamnatin har zuwa zabe na gaba a shekara ta 2017.

Mawallafi Umaru Aliyu

Edita: Saleh Umar Saleh