1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi sabon shugaban majalisar bishop na Jamus

March 12, 2014

Kardinal Reinhard Marx, da aka zaba a yayin taron bishop-bishop da ke gudana a birnin Münster, zai maye gurbin Archbishop Robert Zollitsch mai shekaru 75.

https://p.dw.com/p/1BOlR
Reinhard Marx Präsident Bischofskonferenz PK 12.03.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

An zabi Kardinal Reinhard Marx na yankin München-Freising a matsayin sabon shugaban taron manyan bishop bishop na darikar Roman-Katolika da ke nan Jamus. Kardinal Marx, da aka zaba a yayin taron bishop-bishop da ke gudana a birnin Münster, zai maye gurbin Archbishop Robert Zollitsch mai shekaru 75 kuma daga birnin Freiburg a dalilan tsufa. Tun daga shekara ta 2008 ne dai ya kasance archbishop, kafin a shekara ta 2010 tsohon Paparoma Benedikt na 16 ya dauke shi a kwalejin kardinal. Mai shekaru 60 da haihuwa, Kardinal Reinhard Marx ya kasance daya daga cikin shugabanni lura da batutuwan da suka danganci rayuwar jama'a na majalisar bishop-bishop a nan Jamus, kuma shi ne shugaban hukumar shugabannin darikar Roman-Katolika na Turai. A watan Afrilun shekara ta 2013 ne dai, Paparoma Francis ya nada shi da wasu kardinal guda 7 a matsayin masu ba shi shawara kan gudanar da darikar. Kazalika a wannan Asabar da ta gabata ne dai, Paparoman ya sanar da nadin Kardinal Reinhard Marx a matsayin mai kula da sabuwar majalisar kula da kudaden majami'ar.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Pinado Abdu-Waba