1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi sojin Najeriya da cin zarafin mutane a Filato

Abdullahi Maidawa Kurgwi/ASMay 4, 2015

Rahotanni daga jihar Filato a tsakiyar Najeriya na cewar soji sun hallaka fararen hula a wani sumame da suka kai wasu kauyuka inda wasu mahara suka kashe sojoji shidda.

https://p.dw.com/p/1FJuR
Nigeria Soldaten Offensive gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/J. Penney

Wannan lamari dai ya faru ne bayan da sojojin na Najeriya su ka bayyana cewar sun kai sumame don kakkabe waddan da suka bayyana a mastayin maharan da ke addabar mutanen wasu kauyuka a yankin Wase da kuma kauyukan da ke kan iyakar jihar Taraba da Filato. Bayan kashe-kashen da maharan suka yi rahotanni sun ce maharan sun kashe soji shidda baya ga wasu hudu da suka bace da kuma makaman sojojin da suka kwace.

Wannan lamari dai ya faru ne a kauyen Ungwar Nanmi, kamar yadda kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Filato Kyaftin Ikedechi Iweha ya shedawa DW inda ya ke cewar "maharan sun kashe mata da yara da ma sojojin shida, ka na suka lalata sassan jikinsu don haka muke cigaba da kai musu samame don kuwa har yanzu ba'a san inda maharan suka shiga ba".

Tschad Boko Haram greift Ngouboua an
Baya ga kisan farern hula da aka zargi sojin da yi, an kuma ce sun kone gidajen mutaneHoto: Reuters/M. Nako

To sai dai yayin da sojin ke cewar sun kai sumamen da nufin murkushe maharan da suka yi wannan aika-aika, a hannu guda wata majiya ta shaidawa wakilin DW a Jos cewar sojin sun afkawa mutanen da ba su ji ba su gani ba har ma aka bada labarin rasuwar mutane 50 da kone gidaje da dama.

Sai dai kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Filato din Kyaftin Iweha ce "ban san wannan magana ba kuma ba gaskiya ba ne. Duk wuraren da mu ka kai samamen tun farko mun ce jama'a su kaurace musu, don haka yanzu babu wanda zai ce mun kashe mutane kamar wannan adadin, mutane dai sun kwantar da hankali idan mun gama za a yi karin bayani."

Nigeria Entführungen durch Boko Haram in Chibok
Mutane da dama yanzu haka na gudun hijira a kauyuka makota don tsira da ransuHoto: DW/A. Kriesch

Wannan hali da ake ciki dai ya sanya mutanen da ke zaune a wuraren da lamarin ya shafa wanda suka hada da kananan hukumomin Wase da kuma Langtang ta Arewa kauracewa matsugunansu inda suke zaman gudun hijira a wasu yankunan. Dama dai an jima ana zargin sojin Najeriya da keta alfaramar bani Adama a irin aiyyuka na wanzar da zaman lafiya da su ka yi a sassa daban-daban na kasar, zargin da suka sha musantawa.