1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da gumurzu da 'yan Al-Shabab a Kenya

September 22, 2013

Sojin Kenya na ci gaba da gumurzu da 'yan Al-Shabab din da suka yi garkuwa da mutane a wata cibiyar kasuwanci da ke Nairobi, babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/19lti
A Kenyan army soldier keeps guard in an armoured carrier vehicle, at the Westgate Shopping Centre in Nairobi September 21, 2013. Gunmen stormed the shopping mall in the Kenyan capital Nairobi on Saturday, killing at least 30 people including children and sending scores fleeing in panic, in an attack claimed by the Somali Islamist group al Shabaab. Shooting continued hours after the initial assault as troops surrounded the Westgate mall and police and soldiers combed the building, hunting the attackers shop by shop. A police officer inside the building said the gunmen were barricaded inside a Nakumatt supermarket, one of Kenya's biggest chains. REUTERS/Noor Khamis (KENYA - Tags: CIVIL UNREST MILITARY)
Hoto: Reuters

Rahotanni daga Nairobin Kenya na cewar jami'an kasar Isra'ila na taimaka wa takwarorinsu na Kenya don kubutar da mutane da 'yan Al-Shabab suka yi garkuwa da su a cibiyar kasuwancin nan ta Westgate inda suka killace tun a ranar Asabar har suka hallaka mutane 59 ciki har da 'yan Burtaniya uku kamar dai yadda ofishin harkokin wajen kasar ya bayyana.

Kamfannin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewar tallafin na jami'an na Isra'ila ya taimaka wajen ci gaba da kubutar da mutane daga cibiyar sai dai rahotanni na cewar har yanzu akwai kimanin mutane 30 da 'yan bindigar ke rike da su.

A daura da wannan kuma, rundunar sojin kasar ta Kenya ta ce ta kara yawan sojinta kuma sun yi wa cibiyar kasuwancin kawanya yayin da wasu sojin da dama su ma suka kutsa kai cikin ginin da nufin kawo karshen garkuwar.

Nan gaba kadan ne dai ake sa ran shugaban kasar Uhuru Keyatta zai yi jawabi ga al'ummar kasar, yayin da mataimakinsa William Ruto ya bukaci da a dage shari'ar da ake masa a kotun ICC da ke birnin The Hague don komawa gida ya dafa wa shugaban.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal