1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da samu hare-hare a Najeriya

April 29, 2014

'Yan bindiga dauke da muggan makamai sun hallaka mutane uku a Jihar Adamawa ta Najeriya

https://p.dw.com/p/1Bqps
Nigeria Flüchtlinge aus Borno
Hoto: DW

Lamarin dai ya auku ne a wani kauyen da ake kira Gubla da ke karamar hukumar Madagali, a Jihar ta Adamawa, wanda a yanzu ta ke cikin jihohin da aka azawa dokar ta-baci.

Harin wanda aka kai ba tare da fuskantar turjiyar jami'an tsaro ba, ya zo ne a dai dai lokacin da tsamin dangantaka tsakanin gwamnan jihar Murtala Nyako da fadar shugaban ke daukan sabon salo. An janye mafi yawan jami'an tsaron da ke kare gwamnan sakamakon rashin jituwar.

Yankin arewacin kasar ta Najeriya na fuskatar hare-hare daga 'yan bindiga, inda yanzu haka ake zargin kungiyar Boko Haram masu kaifin kishin addinin Islama, da garkuwa da 'yan mata kusan 200 'yan makaranta, wadanda ake zargi 'yan bindigan na Boko Haram za su amfani da su a matsayin matansu, wajen yi musu fyade.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman