1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da taya Obama murnar sake zabensa

November 7, 2012

Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck da wakilan kungiyar TarayyarTurai da kungiyar tsaro ta NATO da 'yan siyasa na ketare su taya shugaba Obama murnar sake zabensa.

https://p.dw.com/p/16eXX
Hoto: dapd

Shugaban na kasar Jamus cewa ya yi kasashensu biyu wato Amirka da Jamus za su ci gaba da mutunta juna a dangatakarsu. Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle shi kuma a nasa bangaren ya kyautata fatan ci gaba da yin hadin-gwiwa da Amirka bayan sake zaben Shugaba Obama yana mai sa ran ci gaba da shirin wargaza makaman kare dangi. Westerwelle ya fadi haka ne a cikin jawabin da ya yi a birnin New York inda yake ziyara. Ya ce ko da ya ke an samu ci gaba a manufar wargaza makaman kare dangi a shekaru biyun da suka gabata, to amma ana bukatar kara mai da hankali ga wannan batu. A don haka ya yi kira ga kasashen Amirka da Rasha da su yi aiki tare wajen ci gaba da shirin kau da makaman kare dangi domin tabbatar da tsaro a fadin duniya.

Westerwelle ya kuma yi kira da a samar da walwalar cinkayya tsakanin kasahen Turai da Amirka.To sai dai ga baki daya babu wani sauyi da ministan harkokin wajen na Jamus ke sa ran gani a manufofin Amirka akan ketare.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal