1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni na 29.11.2021

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 29, 2021

Da yammacin wannan Litinin ake sa ran sanar da wanda zai lashe kyautar shahararren dan kwalllon kafa na duniya wato Ballon d'Or a birnin Paris na kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/43dGa
Ballon d'Or
Hoto: AFP/T. Samson

Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan dan kasar Poland da ke buga wa kungiyar Bayern Munich ta Jamus, Robert Lewandowski na daga cikin wadanda ake kyautata zaton zai lashe kyautar ta bana. Tun dai a bar ne aka sa ran Lewandowski zai lashe kyautar, sai dai aka dage bikin bayar da ita sakamakon annobar coronavirus da duniya ta tsinci kanta a ciki. 

FC Bayern Muenchen | Robert Lewandowski
Lewandowski na daga cikin wadanda ake kyautata zaton lashe kyautar Hoto: Sven Simon/imago images

Kasashen Birtaniya da Croatia sun samu nasarar zuwa wasan dab da na kusa da na karshe wato quarter-finals a gasar kwallon Tennis ta duniya Davis Cup, bayan da suka samu nasarar a rukunin da suke buga wasan. Sai dai kasar Ostiraliya da ta lashe gasar har sau 28 ba ta ji da dadi ba, domin kuwa ta gaza kai bantenta. Birtaniyan dai ta asamu nasara ne a kan Jamhuriyar Cek, inda ta dara Faransa a maki. Birtaniya da ke a matsayi na 25 a jerin kasashen duniya da suka kware a kawallon na Tennis, ta lashe wasanninta hudu a jere kafin kuma ta fadi wasanni biyar a jere. a yanzu dai akwai yiwuwar Birtaniyan za ta fafata ne da Jamus a wasan na dab da na kusa da na karshe yayin da Croatia za ta kara da Italiya.

Akwai yiwuwar shahararren dan wasan kwallon Tennis na duniya Novak Djokovic ba zai fafata a gasar Tennis ta Australian Open da ke tafe a watan Janairun shekara mai zuwa ta 2022 ba, sakamakon dokokin tilasta mahalarta gasar su yi allurar riga-kafin coronavirus. Rahotanni sun nunar da cewa Djokovic mai shekaru 34 a duniya yaki cewa uffan dangane da batun ko ya yi riga-kafin corona ko kuma bai yi ba. sau tara, dan kasar Sabiyan Djokovic ke lashe gasar ta Australian Open.

US Open Tennis Novak Djokovic Niederlage
Ana zargin Djokovic da kin yin riga-kafin coronaHoto: Elise Amendola/AP Photo/picture alliance

'Yan wasan kungiyoyoin kwallon zari ruga wato Rugby na Ireland Munster da Cardiff sun gaza barin kasar Afirka ta Kudu a Lahadin karshen mako kamar yadda aka tsara a baya, sakamakon kamuwa da annobar corona da suka yi. Kungiyar Cardiff ta bayyana cewa 'yan wasanta biyu sun kamu da sabon nau'in corona na omicron da aka gano a Afirka ta Kudun, yayin da Kungiyar Munster ta ce dan wasanta guda ya kamu koda yake ba ta bayyana ko sabon nau'in ne ko akasinsa ba kawo yanzu.

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF, ta kasance hukumar wasanni ta farko da ta fito fili karara ta nuna goyon bayanta a hukumance kan gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya World Cup duk bayan shekaru biyu, kamar yadda ake gudanar da gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka wato Africa Cup of Nation. Hukumar dai ta bayyana goyon bayan ne a yayin wani taro na ba zata da ta gudanar a kasar Masar.

Fußball Bundesliga | 1. FC Köln - Borussia Mönchengladbach | Fans
FC Kolon ta lallasa Mönchengladbach da ci 4-1Hoto: Dean Mouhtaropoulos/Getty Images

A karshen mako an fafata a mako na 13 na kakar Bundesliga Jamus ta bana, inda a ranar Jumma'ar da ta gabata kungiyar kwallon kafa ta Stuttgart ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Mainz da ta kai mata ziyara da ci biyu da daya. A wasannin da aka gudanar ranar Asabar kuwa, Kungiyar Herthe Berlin ta yi kunnen doki daya da daya da kungiyar kwallon kafa ta Augsburg. VfL Bochum kuwa ta bai wa Freiburg kashi ne da ci biyu da daya kana Greuter Fürth ta kwashi kashinta a hannun kungiyar kwallon kafa ta Hoffenheim da ci shida da uku. Borussia Dortmund ta bi Wolsfburg har gida, ta kuma lallasa ta da ci uku da daya kana Bayern Munich ta lallasa Arminia Bielefeld da ci daya mai ban haushi. Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta FC Cologne ta karbi bakuncin Borrussia Mönschengladbach ne tare da caskara ta da ci hudu da daya.

A wasannin da aka kara a jiya Lahadi kuwa, Eintracht Frankfurt ta lallasa Union Berlin da ci biyu da daya, Leverkusen ta  bi RB Lepzig har gida ta kuma lallasa ta da ci uku da daya. A yanzu haka dai, Bayern ke saman tebur da maki 31 yayin da Borussia Dortmund ke biye mata a matsayi na biyu da maki 30 sai kuma Leverkusen a matsayi na uku da maki 24.

A gasar Premier League ta Ingila kuwa a karshen mako, Manchester City ta caskara West Ham da ci biyu da daya kana Liverpool ta lallasa Southhampton da ci hudu da nema. An dai tashi kunnen doki daya da daya a wasa tsakanin Manchester United da Chelsea kana Arsenal ta lallasa Newcastle da ci daya mai ban haushi. Astonvilla ta lallasa Crystal Palace da ci biyu da daya. Tarin dusar kankara ta tilasta dage wasa tsakanin Burnley da Tottenham, kasa da sa'a guda kafin su fara barje gumi.  

Matakin dage wasan dai ya biyo bayan gaza kwashe dusar kankarar mai tarin yawa da ke sauka cikin sauri kamar yadda ake kwasheta. A wani labarin kuma, kungiyar Manchester United ta bayyana Ralf Rangnick a matsayin mai horas da 'yan wasanta na wucin gadi. Rangnick dai zai maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer da United din ta sallama sakamakon gaza yin katabus a waasanni da dama da kungiyar ta buga a bana.