1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gudanar da zaɓen 'yan majalisun dokoki a Ingila

Abdourahamane HassaneMay 7, 2015

Sama da mutane miliyan 35 waɗana aka yi rejista ake sa ran za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen.

https://p.dw.com/p/1FM2F
Großbritannien Wahlkampf 2015 Ed Milliband
Ed Milliband jagoran jam'iyyar masu nema sauyi BirrtaniyaHoto: AFP/Getty Images/O. Scarff

Zaben wanda hasashe na ra'ayoyin jama'a ke nuna cewar za a yi kunen doki tsakanin manyan jam'iyyun siyasar ƙasar, na 'yan mazan jiya ta David Cameron da kuma masu ra'ayin kawo sauyi ta Ed Milliband.

Inda babu wata jam'iyya da ta samu rinjaye dole ne sai ta nemi ta yi ƙawance da wasu ƙananan jam'iyyun.Ƙasar ta Ingila dai na bin tsarin mulkin mai ruwa biyu wanda firamnistan ke da cikakken iko.Kuma jam'iyyar da ta samu nasara a zaɓen ita ce za ta naɗa sabon firaminista wanda zai girka gwamnati.