1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana shirin ladabtar da Kiir da Machar

April 25, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ta yi alkawarin ladabtar da bangarorin gwamnatin Sudan ta Kudu da na 'yan tawaye da ke yaki da juna idan suka ki gaggauta yin sulhu tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/1BoDF
Hoto: Reuters

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi barazanar kakaba wa bangarori biyun nan da ke gaba da juna a Sudan ta Kudu takunkumi, idan ba su kawo karshen zub da jini da suke ci gaba da yi a kasar ba. Cikin wata sanarwar da ya fitar a birnin New-York, kwamitin ya dora alhakin kashen-kashen fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba na birnin Bentiu da ke arewacin kasar, a kan shugaban Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Da farko dai kasashen Amirka da kuma Faransa sun so a kakaba wa Kiir da kuma Machar takunkumi ba tare da bata lokaci, amma kuma yunkurin nasu ya ci tura. Sannan kuma kasar ta Faransa ta nemi kotun hukuntamanyan laifukan yaki ta duniya ta gudanar da bincike kan ta'asar da ake tafkawa a Sudan ta Kudu.

Tuni dai 'yan tawaye da Machar ke shugabanta suka nesanta kansu daga zargin da aka yi musu na marar hannu a kashe-kashen fararen hula, inda suka dorashi a kan bangaren gwamnatin Kiir .Rahotanin da ke zuwa mana daga Juba babban birnin Suda ta Kudu sun nunar da cewa 'yan tawaye sun yi nasarar kame birnin da ya kunshi akasarin rijiyoyin mai da kasar ta kunsa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu