1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana shirin mika jami'an FIFA ga Amirka

Mouhamadou Awal BalarabeSeptember 17, 2015

Switzerland za ta mika wasu manyan jami'an FIFA ga Amirka don su fuskanci shari'a bisa zarginsu da ake yi da cin hanci da kuma karbar rashawa.

https://p.dw.com/p/1GYGk
Anklage gegen Fifa Funktionäre Portrait-Kombo
Hoto: picture-alliance/epa

Kotun kasar Switzerland ta amince a tasa keyar wasu daga cikin manyan jami'an hukumar Kwallon Kafa ta Duniya zuwa Amirka, bisa zarginsu da ake yi da marar hannu a badakalar cin hanci da kuma karbar rashawa. Daga cikin wadanda wannan mataki ya shafa har da tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta yankin kudancin Amirka Eugonio Figueredo da kuma wasu manyan jami'an FIFA guda shida. Wannan matakin dai shi ne irinsa na farko da Switzerland ta dauka tun bayan barkewar rikicin shugabanci a hukumar ta FIFA.

Manyan jami'an shida na da kwanakki 30 na daukaka kara idan ba su amince da matakin da kotu ta dauka ba. A ranar 27 ga watan Mayu ne aka kama Figueredo a birnin Zurich saboda ana zarginsa da karbar toshiyar makudan kudade game da shirin daukar bakwanci gasar kasashen nahiyar kudancin Amurka ta Copa America.

,