1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ankashe masu zanga-zanga 50 a Kwango

Abdul-raheem HassanSeptember 20, 2016

Jam'iyyun adawa a kasar Kwango sun yi kira gamagoya bayansu da su fito domin ci gaba da fafutuka na nuna kin jinin gwamnatin shugaba Joseph Kabila.

https://p.dw.com/p/1K5Cb
Demokratische Republik Kongo Protest Opposition in Kinshasa
Hoto: Reuters/K. Katombe

Rahotanni daga kasar Kwango na cewar adadin wadan da suka rasa rayukansu a wata arangama tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro ya haura 50, masu zanga-zanagar dai sun gudanar da gangamin ne a Kinshasha babban birnin kasar da nufin matsa wa shugaba Josesp Kabila lamba domin a bayyana jadawalin gudanar da zabubuka a kasar.

Gamaiyyar jam'iyyun adawa a kasar Kwango, sun yi magoya bayansu da su fito dan ci gaba da fafutuka na nuna kin jinin gwamnatin shugaba Joseph Kabila wanda wa'adin mulkinsa ke shirin kawo karshe. A shekara ta 2001 ne dai shugaba Joseph Kabila ya dare karagar mulkin kasar Kwango wanda yanzu ya ke nuna alamun neman wa'adi na biyu.