1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annan ya yi maraba da yarjejeniyar Somalia

June 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bust

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma, tsakanin shugabannin Somalia masu gaba da juna. Annan ya bayyana yarjejeniyar wadda aka kulla a Khartoum babban birnin Sudan tsakanin gwamnatin wucin gadi da kungiyar kotunan Islama da cewa wata nasara ce ta farko wajen kawo karshen tashe tashen hankula a Somalia. Babban sakataren na MDD yayi kira ga sassan biyu da su ci-gaba da tattaunawa don samar da zaman lafiya da yin sulhu tsakanin al´umar kasar baki daya. A cikin yarjejeniyar dai gwamnatin wucin gadi da kungiyar kotunan shari´a sun yarda su amince da juna tare da tsagaita wuta, inji kungiyar kasashen Larabawa wadda ta dauki nauyin shirya taron. A farkon wannan wata na yuni sojojin sa kai na Islama suka kwace birnin Mogadishu.