1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin warare rikicin Isra'ila a Falasdinu

Abdourahamane Hassane
May 25, 2021

Sakataran harkokin wajen na Amirka Antony Blinken ya isa a birinin Tel Aviv na israila a wani mataki na rangadi a yankin gabas ta Tsakiya da nufin samar da shirin tsagaita wuta tsakanin Isra'ilan da Falasdinu.

https://p.dw.com/p/3ttcu
US Antony Blinken in Israel mit Gabi Ashkenazi in Tel Aviv
Antony Blinken tare da ministan harkokin waje na Isra'ila Gabi Ashkenazi Hoto: REUTERS

Atony Blinken wanda zai gana da da firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma jagoran Falasdinawa Mahmud Abbas. zai  yi kokarin jadadda musu muhimmanci dakatar da fadan da sasan biyu ke gwabza kusan kwanaki goma wanda a ciki aka samu asarar rayuka mai dimbi yawa. Sai dai kawo yanzu duk da irin yunkurin diplomasiyar da ake ci gaba da yi ana ci gaba da yin tashin hankalin tsakanin bangarorin biyu musammun ma a yankin zirin gaza da ke a karkashin ikon Hamas