1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Arangama tsakanin dakarun gwamnati da yan tawaye a Niger

March 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuQp

Rahotani daga Jamhuriya Niger, sun ce sojojin gwamnati sun hallaka a ƙalla mutane 5 ɗauke da makamai a wata aranga da su ka gwabza a yankin Uraren na gudumar Arlit , da ke tazaza kussan kilomita 1300 da Niamey babban birni.

Sannan sun ƙwato makamai da harsasai masu yawa, da kuma motoci masu shiga rerai.

A cewar sanarwar opishin ministan tsaro, babu soja ɗaya na gwamnati da ya rasa ran sa a cikin wannan faɗa.

Makamancin wannan arangama, ta wakana ranar 8 ga watan februaru da mu ke ciki , a yankin Iferuan na Jihar Agadaz.

Wata ƙungiyar tawaye mai suna MNJ ta ɗauki alhakin kai wannan hare-hare.

Ƙungiyar na buƙatar a naɗa yan ƙabilar abzinawa a manyan muƙamai na gwamnati, sannan a kyauattata rayuwar al´ummomin yankin abzinawan, wato jihar Agadaz, da ya kunshi albarakatun Uranium.

Saidai har yanzu gwamnatin Niger, ba ta ɗauki ƙungiyar MNJ ba, a matsayin ƙungiyar tawaye, ta na dangata membobin ta kawai, da shegun gari, yan fashi da makami.