1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asarar rai sakamakon yajin aiki a Bangladesh

October 27, 2013

Rahotanni sun ce mutane hudu sun rasu sakamakon rikicin da aka yi tsakanin masu goyon bayan da wanda ba sa goyon yajin aikin da aka fara a Bangladesh.

https://p.dw.com/p/1A6vN
Police officers try to detain a man who was suspected of throwing a crude bomb at police in Dhaka October 26, 2013. Pro-strike activists threw crude bombs, vandalized and set fire on at least thirteen vehicles as more than fifty people were injured in Dhaka. Bangladesh Nationalist Party (BNP) and it's allies called for a three day countrywide strike from Sunday, demanding a caretaker government, local media reported. REUTERS/Andrew Biraj (BANGLADESH - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
An dai yi tarzoma a lokacin yajin aikinHoto: Reuters

A kalla mutane hudu ne rahotanni suka ce an kashe a kasar Bangladesh bayan da 'yan adawar kasar suka fara wani yajin aiki na tsawon sa'o'i sittin don matsin lamba wajen ganin an samar da gwamnatin rikon kwarya ta 'yan ba ruwanmu da za ta sanya ido wajen gudanar zabukan kasar da ke tafe a cikin watan Janairun badi.

Biyu daga cikin mutane da suka rasu dai magoya bayan jam'iyyar Awami League ce wadda ke mulkin kasar kuma sun rasa rayukansu ne bayan da masu goyon bayan yajin aikin da ke goyon bayan jam'iyyar BNP suka far musu, yayin da sauran mutune biyun suka rasu a wata arangama tsakaninsu da 'yan sanda.

Yajin aikin dai yanzu haka ya sanya al'amura a kasar sun tsaya cik, inda makarantu da shaguna da sauraran wuraren kasuwanci musamman a Dhakha fadar gwamnatin kasar suka kasance a rufe.

A ranar Asabar dai ta wayar tarho firaminista Sheikh Hasina ta roki tsohuwar firaministar kasar Khaleda Zia wadda jam'iyyarta ta BNP ke jagorantar yajin aikin da su jingine wannan matsayi da suka dauka sai dai Mrs. Zia din ta ce babu gudu babu ja da baya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal