1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku: Za mu maido da tsaro a Zamfara

February 4, 2019

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a babbar jam'iyyar adawa PDP Alh. Atiku Abubakar ya je yakin neman zabe a jihar Zamfara, jihar da jam'iyyar PDP ke muradin karbar mulki sakamakon rikicin jam'iyyar APC me mulkin jihar.

https://p.dw.com/p/3ChvJ
Nigeria, ehemaliger Vizepräsident Atiku Abubakar
Hoto: Getty Images/P.U.Ekpei

An dai kai ga ya mutsa gashin baki tsakanin jam'iyyar APC mai mulkin Zamfara da hukumar zaben INEC wanda har ta kai ga ba su da 'yan takara. Wannan ziyarar yakin neman zabe dai da Atiku Abubakar ya kai a jihar ta Zamfara na zuwa ne lokacin da shugaban kasar ta Najeriya Muhammadu Bahari ya dage ziyarar ta sa a jihar wanda ake hasashen bai rasa nasaba da rikicin jam'iyyar APC a jihar.  Atiku Abubakar ya samu tarbar daga dinbim magoya baya na jam'iyyar PDP inda ya yi alkawarin samar da tsaro da inganta harkokin noma.

Bello Muhd Matawalle shi ne dan takarar gwamnan a jihar Zamfara ya ce yadda al'ummar jihar suka tarbi Atiku alama ce ta nasara sai kuma ya shawarci Jam'iyar APC a jihar da ta dau kaddarar rashin 'yan takara.

Nigeria Präsidentschaftswahl 2015 Atiku Abubakar
Hoto: DW/U. Musa

Kusan dai dukkanin mahalarta taron cikin murna suke musamman suna alakanta hakan da gani za su kama jihar ta Zamfara Sanata Umar Tsauri shi ne sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya ce lokaci suke jira a rantasar da su.

Dukkanin wanda ya yi magana a wurin wannan taro  na zuwan Atiku  a jihar ta Zamfara, ya kan yi maganar rashin 'yan takarar APC a jihar sai dai a cewar gwamnan jihar Abdul-aziz Yari Abubakar ya zama wajibi hukumar zabe ta sanya 'yan takarar APC na jihar kasancewar babu wata hujja ta hana su takara.

Al'umma dai sun bayyana ra'ayoynsu mabanbanta a dangane da zuwan na Atiku inda da dama suka nuna fata na ganin ya kai labari a zaben shugaban kasa da dan takararsu ta gwamna. Atiku dai ya je jihar ta Zamfara ne yakin neman zabe bayan ya kammala da jihar Kebbi a ranar Lahadi.