1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku ya bar jam'iyyar APC

Ramatu Garba Baba
November 24, 2017

Bayan share tsawon lokaci ana kai-kawo, yanzu tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fice daga inuwar jam’iyya mai mulki da ya zarga da rashin neman shawara daga dattawa da kuma karancin wakilcin matasa.

https://p.dw.com/p/2oCbW
Nigeria Präsidentschaftswahl 2015 Atiku Abubakar
Hoto: Atiku Media Team

An dai dauki lokaci ana jiran tsamani kafin kai wa ga sabon matsayin da ya kai Atiku Abubakar raba auren da ke tsakaninsa da jam'iyyar APC mai mulki. A wata sanarwar da Atikun ya fitar a wannan Jumma'a, ya zargi shugaban kasar Muhammadu Buhari dama jam'iyyar APC da kama karya da rashin mutunta demokradiya. Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ce bai shiga wata sabuwar jam'iyya ba a yanzu, zai yi nazari ga makomar siyasarsa kafin daukar matakin da ya dace nan gaba a yayin jawabin na sa.

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Hoto: Atiku Media Office

Ana kallon yar da kwallon mangwaron cikin APC a bangaren na Atiku na zama kololuwar wani rikicin cikin gidan da ya kalli kokari na rushe kamfanonin da ya ke takama da su da nufin hana shi tashi a nufin cika burinsa na shugabantar Najeriya a nan gaba kamar yadda masu sharhi ke cewa.Yanzu dai kallo ya koma sama inda ake sauraron mataki na gaba da zai dauka a cikin guguwar da ke kara kadawa ta siyasa da ke nuna irin rikicin da ake fama da shi a cikin manyan jam'iyyu biyu na Najeriya.