1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku ya mayar wa Buhari martani

February 19, 2019

Kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kan babban zaben kasar na ci gaba da fuskantar martani na manya da kuma kananan 'yan siyasa.

https://p.dw.com/p/3Dghj
Nigeria, ehemaliger Vizepräsident Atiku Abubakar
Hoto: Getty Images/P.U.Ekpei

Dan takaran jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa da ke tafe, Atiku Abubakar, ya yi kira ga sojojin kasar da su nesanta kansu da babban zaben Najeriyar da ake sa ran yi a karshen mako, yana mai cewa ba su da rawar da za su taka a harkar zaben.

A wani jawabin da ya yi ta kafar talabijin da aka watsa a yau, Atikun ya kuma soki kalaman da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a jiya Litinin.

Shugaba Buharin ya umurci jami'an tsaro da kada su tausaya wa duk wani da ya yi kokarin kawo cikas ga zaben musamman wadanda za su yi yunkurin sace akwatin zabe.

A cewar Buhari dai duk wanda ya yi yunkurin sace akwatin, zai yi hakan ne a bakin ransa, kalaman kuma da Atiku Abubakar ke cewa irin wannan tsarin sai a mulkin kama-karya irin na soja.

Sai kuma bukatar da Atikun ya yi na hukumar zabe ta nisanci nuna fifiko a zaben.