1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

100810 Afrika Extremismus

August 12, 2010

Bisa dukkan alamu ƙungiyoyin 'yan ta'adda, suna ƙara samun ƙarfi a nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/OlxG
Sojojin Mauretaniya cikin saharaHoto: Mohamed Mahmoud Aboumaaly

Ƙaruwar masu tsananin kishin addinin Islama dake shiga ayyukan ta'addanci a nahiyar Afirka, bawai a kasar Somaliya da yakin kasashen larabawa na yammacin nahiyar kaɗai ta tsaya ba, harma ga wuraren irin su jamhuriyar Nijar. Inda a yanzu batun yake barazana a ga wasu yankuna na jamhuriyar Nijar, musamman inda yan ƙaɓilar Buzaye suke. kuma yana neman yakasance wuri mai haɗari.

Sace mutane da yin garkuwa da su a yankin Sahel, wani abune da a yanzu ya kasance barazana ga baƙi masu yawon buɗe ido, musamman waɗanda suka fito daga kasashen yamma, inda a wasu lokutan akanyi garkuwa da mutanen, harma takan kai ga hallakasu. Hakan ya kawo koma baya ga tattalin arzikin yankin domin duk wani abunda ya shafi kuɗin shiga ta baki masu yawon buɗe ido, ya ragu matuka a yakin da ke tsakiyar Sahara. Mano Agahli wani ɗan ƙabilar Buzayene a jamhuriyar Nijar ya kuma bayyana irin koma bayan yakin yake fiskanta

"Akwai mutane da yawa waɗanda kan kuɗin da masu yawon bude ido ke samarwa suka dogara. Milsali yan kasuwa, da musamman kuma waɗanda ke yiwa bakin jagoranci. Yaƙin tawayen na shekara ta 2007, shi ma kansa ya ƙuntatatwa mutane, duk da cewa akasarinsu basu da hannu a yaƙin"

To sai dai ayyukan tawaye na shekara ta 2007 ya sha bamban da na shekarun baya. Inda aka yi ta kaiwa jami'an yan sanda da sojoji hari. Don haka Mano Agahli yace tawayen na kwannan, bai shafi siyasar ƙabilun Buzaye ba.

"Mutanen da suka shiga faɗar a gaskiya ba Buzaye bane, mayaƙan mutane da ke safarar ƙwayoyi da makamai, waɗanda suke cin ribar a yankin. Sai dai kawai sun laɓe ne da sunan tayawayen Buzaye da aka sani. Sun shiga faɗannen kawai da sunnan za su tallafawa Buzaye, dama yankin Agadas"

Aghali wanda tsohon ɗan majalisar dokokine, ya yi shekaru yana fafitikar ciyar da yankin mutanensa gaba. Amma a faɗarsa, wannan yaƙin tawayen da yafaru a shekara ta 2007, wani mummunan koma bayane ga al'ummarsa ta Buzaye, da yankin baƙi ɗaya. Kuma a ganinsa hakanne ya ƙara haifar da masu ayyukan ta'addanci, a sakamaon talaucin da mutanen yankin suka faɗa.

"Ɗaukacin yankin bashi da tsaro, tsaffin mayaƙan suna warwatse a yankin, kuma suna shirye domin jagorantar wasu ayyuka na daban"

Fortschreitende Wüstenbildung Tuaregs in der Wüste Sahara
Buzaye a tsakiyar SaharaHoto: dpa

Koma dai minene yanzu a fili take ayyukan ta'addanci sun ƙaru a nahiyar Afirka. Misali a arewacin Najeriya ƙungiyar "Boko Haramun" wanda ke ƙiran kanta Alƙa'ida, ta tada hankalin mahukunta, inda ta bullo daga Bauchi ta zuwa wasu sassa na arewacin ƙasar. Idan aka yi misali daga jahar Bauchi izuwa Agadas, akwai filin Allah dake shinfiɗe cikin sahara wanda yakai kilo mita 1000, wanda babu wata hukuma dake iko da shi. A tsakiyar Sahara daga Aljeriya izuwa Nijar ƙungiyar Alƙa'ida tun shekaru huɗu ta fara ayyukanta. A gabacin Afirka kuwa tsagerun Somaliya har sun fara aikawa da masu tada bama bamai a ƙasashe maƙobta, kamar wanda aka gani a ƙasar Yuganda.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Ute Schaeffer

Edita: Umaru Aliyu