1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Azumin Ramadana a cikin kayan soja

July 18, 2013

Daga cikin sojoji dubu 250 dake cikin rundunar sojan Jamus kimanin 1000 Musulmai ne, wadanda a lokacin azumin Ramadana ke kokarin daidaita ayyukansu da azumin.

https://p.dw.com/p/19AEe
Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Ulrike Hummel Wann wurde das Bild gemacht?: 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Kaerne in Unna Bildbeschreibung: Oberfeldwebel Chaouki Aakil: „Dieses Jahr kann ich mitfasten.“
Hoto: Ulrike Hummel

Al'ummar Musulmi a sassan duniya daban-daban nu duniya kan yi azumin watan Ramadana, daya daga cikin shika-shikan addinin Muslunci guda biyar. Musulmai ma a nan tarayyar Jamus na bin sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen gudanar da wannan ibada. Sai dai a bana kasancewa watan na Ramadana ya zo ne a lokacin bazara a kasashen Turai da kuma arewacin Amirka inda tsawon rana kan kai kimanin awowi 19 ga kuma tsananin zafi, ya sa wasu Musulman dake gudanar da sana'o'i masu wuyan gaske ko kuma aikin karfi ke ajiye azumin har sai lokacin da yanayi ke da dan sanyi-sanyi kuma ranar ba ta da tsawo sosai.

Azumin watan Ramadana ba sauki ba ne musamman tsakanin rukunin Musulmai masu gudanar da aikin karfi cikin wannan lokaci na zafi a nahiyar Turai. Daga cikin irin wadannan mutane dai har da sojoji. Alkalumma sun yi nuni da cewa daga cikin sojoji dubu 250 dake a cikin rundunar sojan Jamus ta Bundeswehr kimanin dubu daya Musulmai ne, wadanda a lokacin azumin Ramadana ke kokarin daidaita ayyukansu da azumin, abin da ke zama wani karin nauyi a gare su.

Shawara mai wahala

Staff-Sergeant Chaouki Aakil Musulmi ne a bataliyar dake kula tsarin aikewa da kayaki ta rundunar sojojin Jamus. Shi ne kuma ke kula da aikin jigilar kayaki ga sojojin na Jamus. Shi dai Staff-Sergeant Aakil mai shekaru 30 yayi nuni da cewa daukar mataki da ya dace lokacin da aka shiga wani mawuyacin hali ba zai yiwu ba idan ba bu cikakkiyar natsuwa. Aakil na kuwa fuskantar baranazar shiga wannan yanayi a cikin wannan wata na azumin Ramadana, in da Musulmai da azumin ya wajaba kansu ke kame baki daga hudowar alfijir har izuwa faduwar rana. A duk kuma lokacin da watan na azumin kamar a bana ya zo lokacin bazara a Turai, kauce wa cin abinci da shan ruwa na da matukar wahala, inji Staff-Sergeant Chaouki Aakil na rundunar Bundeswehr sannan sai ya kara da cewa idan aka tura shi aiki a kasar waje kamar Afghanistan a cikin wannan lokaci na azumin to gaskiya zai ajiye azumin domin ba zai iya yi a cikin wannan yanayi ba.

"Musamman idan aka tura ka aiki a kasar waje, yana da matukar wahala domin kana cikin wata bakuwar al'ada da baka saba da ita ba, ga zafi ga kuma aikin karfin da muke yi. Bugu da kari kana nesa da gida, duk wadannan wasu nauye-nauye ne dake tasiri a kan kowane dan Adam. Saboda haka ni kam na yanke ma kaina shawara cewa ba zan yi azumin a cikin irin wadannan kasashe ba, domin ba zan samu isasshen karfi da natsuwar tinkarar wani yanayi na ba-zata da ka iya tasowa ba."

Staff-Sergenat Chaouki Aakil ya kara da cewa a matsayinsa na soja a rundunar Bundeswehr baya ga zafi mai kuna akwai kuma aikin dake karin nauyi a jikinsa da kuma kwakwalwarsa, ga kuma bakuwar kasa da yake a cikinta da yake la'akari da ita.

Bundeswehreinsatztruppe auf Minensuche in Nordafghanistan. Kunduz Kundus Qhunduz, Afghanistan, 21.10.2012
Sojojin Jamus a AfghanistanHoto: picture alliance / JOKER

Yin azumi ko rashin yin sa wani ra'ayi ne mai wuyar dauka ga sojoji Musulmin, wanda a karshe ya rage wa kowane sojan ya dauka wa kansa. A hannu daya dai azumin watan Ramadana dai daya ne daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar wanda kuma yake farilla ga duk baligi namiji ko mace dake da koshin lafiya. A daya hannun kuma yin azumin a cikin wani yanayi mawuyaci ka iya janyo wasu matsaloli na musamman bisa dalilai na kiwon lafiya, inji Michael Faust shugaban manyan likitoci a asibitin jami'ar birnin Kolon.

"Sojojin na gudanar da aiki mai wuya a ketare da kan shafi karfin jikinsu. Suna kuma bukatar cikakkiyar natsuwa domin kaucewa tabka kura-kurai a cikin aiki. Saboda haka ana bukatar shan ruwa sosai. Amma ga abin da ya shafi nau'in abinci mai nauyi, ana iya jurewa na lokaci mai tsawo musamman idan mutum ya ci abinci da asuba ko a lokacin bude baki. Ko da yake bisa dalilai na kiwon lafiya ba a son barin ciki da yunwa lokaci mai tsawo, amma gaskiya ba bu wani damuwa game da hakan. Sai dai shan ruwa yana da matukan muhimmanci a wannan yanayin."

Sassauci ga wani rukuni na jama'a

Wannan dai na ci gaba da zama wani batu ne na radin kai. A wasu lokutan an yi wa Musulman sassauci. Alal misali maras lafiya da matafiyi, mace mai juna biyu ko mai shayarwa da kuma tsofaffi suna iya ajiye azumin sannan su yi ranko ko ciyarwa maimakon yin azumin, inji Erol Pürlü masanin kimiyyar addinin Musulunci kuma mai kula da Musulmi da suka shiga wani hali na damuwa.

"Marasa lafiya da matafiya ka iya ajiye azumi sannan su biya daga baya. Wannan ya kuma shafi mutane masu sana'a mai wuya wadanda bisa dalilai na musamman game da sana'o'in na su ba za su iya yin azumin ba. Suna iya biyan azumin bayan watan Ramadana."

Masanin kimiyyar addinin ya kara da cewa ai manufar azumin shi ne kara wa mutum lafiya amma ba cutar da shi ba.

Erol Pürlü, Dialogbeauftragter des Verbands der Islamischen Kulturzentren e.V. (VIKZ) Copyright: Ulrike Hummel Juli, 2012, Köln
Masanin kimiyyar Islam Pürlü-"Azumi don kara lafiya ne amma ba cutarwa ba"Hoto: Ulrike Hummel

A wannan shekarar dai Staff-Sergeant Chaouki Aakil na aiki ne a barikin soji dake garin Unna. Daga cikin aikin da yake yi akwai watsan motsa jiki na dole da kuma darasin harbe-harbe. Amma azumin bana da ake kame baki tsawon sa'o'i 19 a rana na zama babban kalubale. Hakazalika a cikin watan na Ramadana dole a sake fasalta tsarin aiki da ma lokacin cin abinci na sojoji Musulmai domin a kullum lokacin hudowar alfijir da faduwar rana na canjawa da 'yan mintoci, amma hakan na tafiya ba matsala inji sojan.

"Ko shakka babu yin azumi a cikin rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr yana da matukar wuya, domin wuraren cin abincin na dakarun soja ne inda ake zuwa cin abinci lokacin da aka tsara. Saboda haka dole sai mun yi masu magana tun da farko kafin a ware mana lokaci daban na cin abinci."

Halal amma karlashin dokokin kasa

Rundunar ta Bundeswehr ta kuma tsara irin nau'in abinci da take bayarwa. Alal misali ana ba wa Musulmi abincin da addininsu ya amince da su ci wanda ake sanya masa alamar halal. Sai dai saboda wasu dalilai na dokokin kasa da suka shafi yanka dabba, rundunar ba ta ba wa Musulman naman da aka yanka kamar yadda wasu darikun ke bukata.

Amma idan aka kwatanta da wasu manyan hukumomi ana iya cewa kantin din rundunar ta Bundeswehr yayi nisa wajen ba da la'akari ga bukatun Musulmi, domin a garin Unna ga misali ba a amfani da tukunya ko wani abin girki daya wajen dafa alal misali naman alade ko shanu ko kaza.

Die Bundeswehrärztin Franka Korb (l) sitzt mit anderen Bundeswehrsoldatinnen in der Kantine im Stützpunkt Kinshasa (Foto vom 23.10.2006). Die 32 Jahre alte Rettungsärztin aus Leipzig fliegt im Kongo in den Transporthubschraubern der Bundeswehr mit und soll im Notfall Patienten während des Fluges versorgen. Die etwa 280 Bundeswehrsoldaten, die seit Monaten in ihren weißen Sechs- oder Acht-Mann-Zelten unter Moskitonetzen schlafen, hoffen darauf, dass sie Weihnachten wieder zuhause sind. Bislang ist nicht viel passiert, selbst von Tropenkrankheiten blieben die Soldaten verschont. Foto: Ulrike Koltermann (zu dpa-Reportage "Stichwahl im Kongo - Kongolesen sind gelassen, Bundeswehr angespannt" vom 26.10.2006) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Kantin din Bundeswehr na ba da la'akari da dokokin addiniHoto: picture-alliance/dpa

Idan Aakil ya samu dama ya fi sha'awar yin azumin a tsakanin iyalinsa. Domin ai azumin ba kawai kaurace wa abinci da ruwa ba ne, wata ne mai muhimmanci da kuma lada wajen yin ayyukan alheri da taimaka wa jama'a musamman marasa karfi.

Mawallafa: Ulrike Hummel / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani