1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba za a hana alhazan Najeriya zuwa Saudi ba

September 8, 2014

Mahukuntan Saudi Arabiya sun sake jaddada cewar ba za su dakatar da alhazan tarayyar Najeriya daga shiga kasar don gudanar da aikin hajjin bana saboda cutar Ebola ba.

https://p.dw.com/p/1D8mB
Hadsch Saudi-Arabien
Kimanin alhazan Najeriya dubu 76 ne ake sa ran za su yi aikin hajjin banaHoto: dapd

Mukaddashin ministan kiwon lafiyar Saudi Arabiya din Mohammed Al-Khasheem ne ya tabbatar da hakan, inda ya ke cewar babu wata bukata ta hana Alhazan na Najeriya cigaba da shiga kasar don sauke farali saboda yawan wanda suka kamu da cutar a kasar ba su da yawa don haka ba abin damuwa ba ne.

Baya ga haka mininistan ya kuma ce ma'aikatarsu tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya na yin aiki tukuru don ganin ba a samu bullar cutar ba a kasar musamman ma wajen zaman Mina.

A makonnin da suka gabata ne dai hukumomin Saudiyyan suka ce ba za su baiwa alhazan kasashen da suka hada da Saliyo da Liberiya da kuma Gini izinin shiga kasar ba duba da yadda cutar ta Ebola ta bazu a kasashensu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal