1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba za a sake dage zaben Najeriya ba - Dasuki

February 9, 2015

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro a Najeriya Sambo Dasuki ya ce ba za a sake dage zaben kasar ba.

https://p.dw.com/p/1EYOF
Nigeria Demonstration gegen Verschiebung der Wahl 7. Februar 2015
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Gbemiga

Mai ba da shawara kan tsaron kasa a Najeriya Sambo Dasuki ya fada wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa ba za a sake dage babban zaben kasar fiye da ranar 28 ga watan Maris ba. A lokacin da aka yi masa tambaya ko ana iya sake dage zaben wanda da farko aka shirya yi a ranar 14 ga watannan na Fabrairu, Dasuki ya ce ba za a sake soke ranakun zabubbakan. Dasuki dai ya nemi jami'an hukumar zaben Najeriya da su dage zaben saboda dalilain cewa sojoji ba su iya tabbatar da tsaro a fadin kasar lokacin zaben ba saboda an girke su a yankin arewa maso gabashin kasar don su yaki Boko Haram.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo