1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban hafsan sojojin Israila yayi murabus.

Hauwa Abubakar AjejeJanuary 17, 2007

Dan Halutz ya yi murabus ne daga mukaminsa bisa zargin da ake masa game da yadda ya gudanar da yaki kan Hezbollah

https://p.dw.com/p/Btwb
Dan Halutz
Dan HalutzHoto: AP

Babban hafsan sojin na Israila wanda ya zamo babban jamii na kasar da ya kaddamar da yaki kan Hezbollah,wani tsohon matukin jirgin sama ne,wanda ya kasance sojan sama na farko daya jagoranci rundunar sojin Israila.

Ya kuma yi murabus ne yana mai cewa dole ne ya dauki alhakin yakin da suka kaddamar kan Hezbollaha Lebanon,inda kwallaiya bata biya kudin sabulu ba.

A watan yuni na 2005 lokacinda aka rantsarda Dan Haluzt,da ake ganin mutum ne da alamuransa ba sani ba sabo,jamaa da dama sunyi maraba da nadin nasa a matsayin wanda shi kadai ne zai iya magance barazanar da Iran take da shi kan Israila.

Amma sai gashi yayi murabus game da suka da akeyi masa kan yadda ya shirya yaki kan Hezbollah,wanda har yanzu baa kwati sojoji biyun da aka ce an kaddamar da yakin domin kwato su ba.

Dan asalin kasar Iran,Haluzt an haife shine a 1948 a daidai lokacinda aka kirkiro kasar ta yahudawa,ya shiga aikin soji a 1966 inda yayi suna da kara saamun girma saboda bajimta da ya nuna a lokacin yakin Yom Kipur na 1973.

A 2002 ya jagoranci harin bam na 2002 kan shugaban Hezbollah inda mutane 15 suka rasa rayukansu.

Batu daya janyo suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama,inda har suka shigar da karat a bukatar tsige shi a matsayin babban hafsan sojojin kasar ta Israila bayanda ya baiyana farain cikinsa game da kashe mutane cikin harin daya bada umurni akai.

A yakin da yayi da Hezbollah kuma an zarge shi da maida hankali kan hari ta sama,yayinda dakarun dake kasa basu da isashen horo da kayan aiki,haka kuma cewa an tura su kasar Lebanon din cikin kurarren lokaci.

Yanzu haka dai firaminista Ehud Olmert yace ya karbi murabus din na Haluzt cikin bakin ciki da rashin jin dadi.

Da murabus din na Haluzt,akwai yiwuwar matsawa ministan tsaro Peretz da shima ya ajiye aikinsa bisa wannan batu na yaki akan Hezbollah,inda mutane 1,000 suka rasa rayukansu,yawancin kuma fararen hula,Israila a nata bangare tace tayi hasarar mutane 159,118 cikinsu sojoji.

Wani bincike da rundunar sojin kasar tayi karkashin manjo janar Amiram Levine mai ritaye yace shugabanin sojin basu ci nasara ba ta kowace fuska a lokacin yakin.

Ana sa ran cikin wata mai zuwa kuma,komitin bincike karkashin jagorancin tsohon alkali Eliyahu Winograd,zai fito da sakamakon binciken da yayi kan yadda aka gudanar da yayin,inda ake san a zai yi suka ga shugabannin soji dana siyasar Israila.