1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron Majalisar Dinkin Duniya

Gero Schließ / SBSeptember 24, 2014

Matsalolin da ake fama da su yanzu kamar yaki da 'yan ta'adda irin su kungiyar IS, da cutar Ebola da yadda za a tinkari Iran, za su mamaye babban taron na bana.

https://p.dw.com/p/1DKaf
UN Hauptquartier New York Gebäude
Hoto: Emmanuel Dunand/AFP/Getty Images

Fiye da shugabannin kasashen duniya 140 suke halartar babban taron na Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara, inda yaki da kungiyoyi masu matsanancin ra'ayi irin su kungiyar IS mai neman kafa daular Islama a Iraki da Siriya, gami da cutar Ebola da ke yaduwa a kasashen yammacin Afirka da kuma batun nukiyar Iran za su kasance kan gaba wajen daukar hankali mahalarta taron.

Ministan harkokin wajen kJamus Frank-Walter Steinmeier yana ganin wannan makon na taron babbar mashawartar Majalisar Dinkin a matsayin wata dama ta samar da goyon baya ga sabuwar gwamnatin Iraki.

"Muna goyon bayan sabuwar gwamnatin Iraki, wadda ke neman gyara kuraren da aka tabka a baya."

Ya kara da cewa babban buri shi ne karya duk wani karfin mayakan kungiyar IS, wadanda suka samu goyon bayan 'yan Iraki da suka fusata. Sannan Steinmeier yana fatan ganin samun martanin da ya dace kan lamarin, tare da jaddada aniyar kasar ta Jamus kan ci gaba da bai wa dakarun Kurdawan Iraki makamai, domin ci gaba da fafutukar da suke yi da mayakan IS.

Außenminister
Frank-Walter Steinmeier a BagadazaHoto: picture-alliance/dpa

Muhimmancin Jamus wajen yaki da IS

A ganin Heather Conley masaniya a cibiyar nazarin dubarun yaki ta kasa da kasa da ke birnin Washington, zaman taron Majalisar Dinkin Duniya zai bai wa Amirka damar hada kawancen yaki da kungiyar IS. Amirka dai ke shugabantar Kwamitin Sulhu, inda Shugaba Barack Obama zai yi amfani da wannan dama. Yayin da Jeremy Shapiro na cibiyar Brookigs Institute da ke Washignton ya nunar da mahimmancin Jamus wajen kawance da Amirka.

Michael Werz na cibiyar ci-gaba ta Amirka yana ganin taron majalisar a matsayin wanda zai mayar da hankali kan magance matsalolin da ake ciki, inda ya ce:

"Wannan babban taron na Majalisar Dinkin Duniya zai mayar da hankali kan abin da ya shafe mu daga cutar Ebola zuwa Siriya bisa tambayoyi kan matakan Turai da Amirka, game da rikicin Gabas ta Tsakiya da taimakon dakile masu kaifin kishin Islama."

Kudirin yaki da tsattsaurar akida

Akwai bukatar samun amincewa da kudiri wanda kasashen duniya za su yi aiki da shi wajen dakile 'yan kasashen ketare da ke shiga rikici. A cewar jaridar New York Times akwai mayaka 'yan kasashen ketare fiye da 15,000 da ke fafatawa a rikicin Iraki da Siriya. Fiye da 2,000 sun fito ne daga kasashen Turai, inda wasu daruruwa a ciki daga Jamus.

Yaki da mayakan IS da ke neman kafa daular Islama, gami da rikicin gabashin Ukraine ke daukar hankali, amma yanzu akwai kari da cutar Ebola da take ta'adi a kasashen yammacin Afirka. Kuma tuni cutar ta shiga sahun gaba a wajen taron na Majalisar Dinkin duniya, inda ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nemi ganin kasashe sun kara himma bisa manufar da aka sa gaba.

Ebola Warnung Symbolbild
Ebola na Zaman sabon kalubale ga kasashen yammaHoto: Reuters

"Bayan rikicin IS a fayyace yake cutar Ebola ce a kan tanade-tanaden tattaunawar. Akwai bukatar kasashen duniya su kara azama wajen taimaka wa kasashen da ke karkashin barazana wato kamar Laberiya, da Saliyo, da kuma Guinea da taimakon yadda za a magance wannan cuta."

Steinmeier ya nemi kasashe musamman masu karfi su taimaka da kayan kiwon lafiya da ake bukata na magance cutar ta Ebola.

Wabi babban abin da ya dauki hankali a shekarar da ta gabata yanzu ya sake shiga gaba shi ne batun nukiyar kasar Iran.