1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron ƙasa a Najeriya mai fama da rarrabuwar kai

March 18, 2014

A wannan Talata wakilai da ke halartar babban taron suka fara tattaunawa gadan-gadan tare kuma da yin nazarin ɗaukacin ginshiƙan ƙasar da nufin samar da hanyoyi na ci-gaba da kuma makomar ƙasar.

https://p.dw.com/p/1BRge
Hoto: AMINU ABUBAKAR/AFP/Getty Images

Bayan ƙaddamar da babban taron ƙasa a ranar Litinin, a wannan Talata wakilai 500 na 'yan siyasa da kuma ƙungiyoyin ci-gaban al'umma suka fara shawarari a babban taron na ƙasa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Sai dai ana ganin taron ba zai samu cikakkiyar damar gano bakin zaren warware ɗindim matsalolin da tarayyar ta Najeriya ke fuskanta a yanzu ba. To amma ministan yaɗa labarun Najeriya Labaran Maku ya ce taron zai duba muhimman batutuwa a ɓangarori da dama na ƙasar.

"Mutane da yawa suna cewa akwai gyara, gyaran shi ne yaya za a yi gwamnatin demokraɗiyya ta ƙara inganta ayyukan raya ƙasa, mai zama dangantakar gwamnatin tarayyar da jihohi da kuma ƙananan hukumomi."

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013
Shugaba Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/AP Photo

Najeriya dai na fuskantar ƙalubale masu yawa, musamman na rashin tsaro, inda ko a ƙarshen makon da ya gabata wasu 'yan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyuka da ke jihar Kaduna inda suka hallaka mutane kusan 200. A yankin arewa maso gabashin ƙasar har yanyu ana fama da ta'asar 'yan ƙungiyar nan ta Boko Haram. Duk da dokar ta-ɓaci da shugaban Najeriya Goodluck Jonatha ya kafa a jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe a watan Mayun bara, dubun dubatan mutane ke tserewa daga wannan yanki. A kudancin ƙasar ma shekaru da yawa na aikin haƙo man fetir ya lalata ɗaukacin yankin Niger Delta. Mazauna yankin sun yi asarar abubuwan da suka dogara kai na rayuwa, abin da ya janyo matasan yankin shiga ƙungiyoyin ɗaukar makami.

Yakin zaɓe na gaba da wa'adi?

Murtala Nyako
Gwamnan Adamawa Murtala NyakoHoto: DW/U. Shehu

Wata uku wakilai za su kwashe suna tattaunawa game da matsalolin Najeriya. Sai dai gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya nuna shakku game da samun nasarar taron.

"Me za ma a faɗa wanda ba a faɗa ba? An yi taruka ba sau ɗaya ba sau biyu ba, an ba da shawarwari. Abin da za mu yi yanzu shi ne yaya za mu aiwatar da shawarwarin da aka bayar a baya."

Heinrich Bergstresser dan jarida ne kuma masani a kan zamantakewa ya ce bai yarda taron zai gabatar da wani sabon abu ba. Ya ce bambamcinsa da tarukan baya na lokacin gwamnatocin soji shi ne yanzu ƙasar na bin tafarkin demokraɗiyya ne amma gwamnati ba ajandar taron ne ta saka a gaba ba.

Rarrabuwar kawuna a Najeriya

Niger Kämpfer
'Yan bindigar Niger DeltaHoto: picture-alliance/dpa

"Wannan taron bai da wata manufa a bayyane in ban da ƙoƙarin ɗinke ɓarakar da ke cikin jam'iyyar da ke jan ragamar mulki. Zai zama wani zaure ne na yaƙin neman zaɓe. Wadanda ke son shiga majalisa ko zama gwamnoni za su iya amfani da taron don baje kolinsu, za a kuma biya su maƙudan kuɗaɗe."

A baɗi wato shekarar 2015 za a gudanar da manyan zaɓuka a Najeriya kuma ko shakka babu shugaba Jonathan zai tsaya takara.

Ko da yake ƙungiyoyin al'umma sun jima suna kira da a gudanar da taron sasanta 'yan ƙasa, amma ko su ɗin ma ba su gamsu da sigar wannan taron ba. Wasu daga cikinsu sun bayyana taron da cewa wani lamari ne mai tayar da hankali wanda kuma suka ce yunƙuri ne na karkata hankalin jama'a daga matsalolin da ƙasar ke fuskanta. Yanzu dai an zura ido a ga irin shawarwarin da babban taron zai gabatar da nufin magance matsalolin tarayyar ta Najeriya.

Mawallafa: Philipp Sandner / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar