1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babbar Sallah cikin tsauraran matakan tsaro

October 26, 2012

A ranar Juma'a al'ummar Musulmi a ko ina cikin duniya suka gudanar da bukukuwan Sallar layya, sai dai a wasu wurare a Najeriya an yi bikin cikin yanayi na fargaba.

https://p.dw.com/p/16Xwx
Hoto: Getty Images/AFP

A Kano dake arewacin Najeriya ga misali an gudanar da bikin idin babbar Sallar ne a yanayi na ƙwararan matakan tsaro. To sai dai duk da tsaron bikin sallar ya ɗara na ƙaramar sallar da ta gabata armashi kasacewar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya yi hawan Sallah wanda ya na ɗaya daga cikin bikin hawa da aka saba yi tun lokacin da aka fara shi a 1903.

A jawabin da sarki ya yi bayan matashiya kan muhimmancin layya ya sake jaddada horonsa ga jama'a kan muhimmacin biyayya ga Allah.

Tunawa da Ubangiji a dukkan fannoni na rayuwa

"Muna ƙara gargaɗinku jama'a mu ji tsoron Allah a zahiri da badininmu.Mu bi umarnin ubangiji da kuma gujewa sabonsa.Haka kuma mu kyautata dangantaka tsakaninmu tare da baiwa kowa hakkinsa, mu zauna lafiya da soyayya da junanmu mu baiwa hukumomi haɗin kai. Mu sani cewa zaman lafiya babban abu ne."

Ilmi haɗe da tarbiyya ginshikai biyu ne na ci gaban kowace al'umma kuma su na daga cikin abubuwan da ya kara jadada muhimmancinsu a wannan lokaci.

Ado Bayero Emir von Kano/Nigeria
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado BayeroHoto: Thomas Mösch

"Haka kuma a kula da harkar ilmin yara tare da ba su tarbiyya ta gari."

Waɗannan kalamai tamkar matashiya ce ga hukumar Hisbah ta jihar Kano inda ta shirya aro da masu wuraren da suka saba shirya wasannin Sallah don su faɗakar da su dokokin Hisbah game da bikin.

Malam Abba Sa'id Sufi shi ne Darakta Janar na hukumar.

"Mun gayyato wurare irin inda ake tara yara masu "Amusement Park" da suke wasa da yara suke abubuwansu. To mun nuna musu wannan wuri na yara ne ba za a bar manya su shiga su gurbata tarbiyyar yara ba. Shi gidan zoo wuri ne na maza da mata da yara da manya. To amma an yi kokarin cewa a ware wurin maza dabam wurin mata dabam wurin yara dabam yadda ba zasu ga wata al'ada da za ta canza musu tunaninsu ba.

A jamhuriyar Nijar ma al'ummar musulmin kasar sun bi sahun takwarorinsu na duniyar Musulmi wajan raya wannan rana ta sallar layya. A birnin Yamai shugaban ƙasar Alhaji Mouhamadou Issoufou da mambobin gomnatinsa da ma sauran al'ummar Musulmi sun halarci Sallar idi da aka gudanar a babban masallacin Juma'a na Gaddafi da ke a birnin na Yamai a ƙarƙashin jagorancin limancin na'ibin sheik Umar Ismael shugaabn babbar ƙungiyar addinin Musulunci ta ƙasa wanda Allah Ya yiwa cikawa a farkon wanann mako bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.

Die Wüstenschlachterei
Cin nama na daga cikin abubuwan da suka ɗaukar hankali a lokacin layyaHoto: DW/J.Hannover

Mawallafa: Abdulrahman Kabir/Gazali Abdu Tasawa
Edita Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani