1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu dalilin mayar da Rasha saniyar ware- Steinmeier

Mohammed Nasiru AwalApril 15, 2015

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce ba bu mai sha'awar mayar da Rasha saniyar ware.

https://p.dw.com/p/1F98O
Deutschland Treffen der G7 Außenminister in Lübeck
Hoto: picture-alliance/dpa/AA/M. Kaman

A lokacin da yake magana a karshen taron ministocin harkokin wajen kungiyar G7 a garin Lübeck, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce ba bu kasa ko guda daya memba a cikin kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arziki da ke sha'awar ganin an mayar da Rasha saniyar ware. A shekarar da ta wuce aka kori Rasha daga kungiyar G8 saboda goyon bayan da take ba wa 'yan awaren gabashin Ukraine masu gwagwarmaya da makami. Steinmeier ya ci gaba da cewa hanya daya tilo da Rasha za ta sake shiga kungiyar ita ce aiwatar da yarjejeniyar birnin Minsk tare da kawo karshen rikicin Ukraine. Sai dai ya yi tir da matakin da Rasha ta dauka na sayar wa Iran makamai masu linzami.

"Na yi mamaki da shawarar da Rasha ta yanke na sayar wa Iran makamai. Fatanmu shi ne kawo karshen rikicinmu da Iran. Bayan mun kwashe shekaru 12 muna tattaunawa yanzu akwai damar cimma wani sakamako cikin watanni biyu masu zuwa. Saboda haka ya kamata mu yi takatsantsan ga matakan da zamu dauka yanzu."