1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Badakalar satar bayanai a Jamus

November 5, 2013

Kokarin gayyato Edward Snowden zuwa Jamus na janyo cece kuce ga makomar dangantakarta da Amirka.

https://p.dw.com/p/1ACla
German Greens lawmaker Hans-Christian Stroebele poses for a picture with fugitive former U.S. spy agency contractor Edward Snowden (L) in an undisclosed location in Moscow, October 31, 2013. Stroebele met Snowden in Moscow on Thursday, Stroebele's office said in a statement, and would give details of the meeting on Friday. Snowden passed on an envelope with a letter addressed to the German government, Germany's lower house of parliament, the Bundestag, and to the Federal Public Prosecutor (Generalbundesanwalt). The letter is to be disclosed during a news conference on Friday in Berlin. REUTERS/Handout (RUSSIA - Tags: POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY) ATTENTION EDITORS � THIS IMAGE WAS PROVIDED BY A THIRD PARTY. NO SALES. NO ARCHIVES. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS PICTURE IS DISTRIBUTED EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Bayan ganawar da mukaddashin shugaban 'yan majalisar dokokin Jamus daga jam'iyyar The Greens Hans- Christian Ströber yayi tare da tsohon jami'in hukumar leken asirin Amirka Edward Snowden a Rasha. A yanzu lamarin na ci gaba da janyo cece-kuce dangane da tasirin gayyato jami'in zuwa Jamus domin bada bahasi a binciken da wani kwamiti ke gudanarwa, ko kuma tura wata tawagar Jamus domin ganawa da shi zai yi.

Demonstranten unterstützen am 04.07.2013 vor dem Reichstag in Berlin mit Plakaten den Ex-US-Geheimdienstler Edward Snowden. Snowden hatte die Datenspionage der USA und Großbritanniens enthüllt. Foto: Ole Spata/dpa
Boren neman baiwa Snowden mafaka a JamusHoto: picture-alliance/dpa

Kasancewar Amirka ta bayar da warantin kasa da kasa na cafke Edward Snowden, da ke zama tsohon jami'in hukumar leken asirin kasar, akwai bukatar Jamus ta mutunta wannan yajejeniyar - da zaran ya shigo kasar, domin kuwa tun a shekaru da dama da suka gabata ne Amirka da Turai suka kulla yarjejeniyar da ta shafi waranti na kasa da kasa. Sai dai kuma wani binciken da ofishin kula da harkokin ketare na Jamus ya gudanar, ya gano cewar, ba wai wajibi ne a mutunta wannan yarjejeniyar ba - idan laifin na da nasaba da siyasa.

Dadaddiyar dangantaka a tsakanin Jamus da Amirka

Sai dai kuma lamarin bai fito fili ba dangane da matsayin Snowden, musamman kasancewar bashi mafaka - sharadi ne na zuwansa, wanda kuma a ganin Karsten Voigt, tsohon jami'in gwamnatin Jamus a shirin kawance tsakanin Amirka da Jamus, matsalar za ta shafi alakar da ke tsakanin kasashen:

"Tun bayan gamewar yammaci da gabashin Jamus, da kuma bayan kawo karshen yakin cacar-baka, dangantaka da Amirka ce mafi muhimmancin da Jamus ke da ita da wata kasar da ke wajen tarayyar Turai."

FILE - In this Sept. 6, 2013, file photo, President Barack Obama, right, walks with Germany's Chancellor Angela Merkel prior to a group photo of G-20 leaders outside of the Konstantin Palace in St. Petersburg, Russia. Reports based on leaks from former NSA systems analyst Edward Snowden suggest the U.S. has monitored the telephone communications of 35 foreign leaders. The fact that Merkel was among them has been particularly troubling to many in Europe and on Capitol Hill, given her status as a senior stateswoman, the leader of Europe¿s strongest economy, and a key American ally on global economics, Iranian nuclear negotiations and the Afghanistan war. (AP Photo/Ivan Sekretarev, File)
Merkel da ObamaHoto: picture-alliance/AP Photo

Tushen alakar dai shi ne kariyar da Amirkawa suka bai wa yammacin Berlin a lokacin yakin cacar baka. Hakanan sojojin Amirka sun samar da abinci ga yammacin Jamus yayin da dakarun tarayyar Soviet suka katse hanyar kai musu kayayyakin rayuwar yau da kullum a tsakanin shekara ta 1948 da kuma 1949, kana kuma da gagarumar rawar da Amirka ta taka wajen bunkasa yammacin Turai ciki kuwa harda yammacin Jamus bayan yakin duniya na biyu. Tun lokacin ne kuma dangantakar siyasa da na tattalin arziki tsakanin kasashen biyu ke ci gaba da bunkasa. A cewar Farfesa Thomas Hünter masanin manufofin ketare da na kasa da kasa a jami'ar Köln da ke nan Jamus, tun a shekaru 10 da suka gabata ne rabon da a samu koma baya a dangantakar, wato sa'ilin da Jamus ta kaucewa goyon bayan Amirka a yakin Iraqi na farko.

Mafita ga Jamus da Amirka a rikicin bayanan sirri

Sai dai a cewar Wolfgang Ischinger, tsohon jakadan Jamus a Amirka, duk wani yunkuri na gayyato Snowden zuwa Jamus, zai dagula sabanin da ya sake kunno kai ne kawai:

"Mai yiwuwa Amirkawa su kalli abin a matsayin cin fuska, kamar dai yadda 'yan siyasa a Jamus ma ke ganin satar bayanai ta wayar salularsu da Hukumar Leken Asirin Amirka ta yi a matsayin cin fuska."

Tsohon jakadan dai ya ce tunda jaridar Der Spiegel ta nan Jamus, ta ruwaito shirin da wasu 'yan majalisar dokokin Amirka ke yi na zuwa nan Jamus domin dinke barakar diflomasiyyar, abu ne da ya kamata sassan biyu su ci gajyarsa:

"Abu ne mai muhimmanci maido da yardar da ke tsakanin juna domin gyara barnar da ta afku, wanda zai amfani Turai da Amirkar."

Tattaunawa ce kawai a ganin masana, za ta iya saukaka kurar da ta taso sakamakon leken asirin da Amirka ke yi wa Jamus, kamar yadda tsohon jami'in hukumar Edward Snowden ya kwarmata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Pinado Abdu Waba