1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure 28 sun halaka a gabar ruwan Italiya

October 5, 2016

Jami'an kula da gabar ruwan kasar Italiya sun sanar a wannan Laraba da yin nasarar ceto bakin haure da 'yan gudun hijira dubu hudu da 655 daga tekun Baharum a tsawon yinin Talatar jiya kadai

https://p.dw.com/p/2QtgP
Libyen - Flüchtlinge auf überladenem Boot warten auf Rettung
Hoto: Getty Images/AFP/A. Messinis

Jami'an kula da gabar ruwan kasar Italiya sun sanar a wannan Laraba da yin nasarar ceto bakin haure da 'yan gudun hijira dubu hudu da 655 daga tekun Baharum a tsawon yinin Talatar jiya kadai, tare kuma da tsamo gawarwakin mutane 28 a cikin ruwan tekun. 

Sun kuma kara da cewa sun kai dauki fiye da sau 30 ga jiragen bakin hauren a ranar Talatar ta jiya kadai. A ranar Litanin kadai kuma jiragen ruwa 40 dauke da 'yan gudun hijira sama da dubu shida da ke kokarin tsallakwa zuwa Turai ne, jami'an gabar ruwan kasar ta Italiya suka yi nasarar cetowa. 

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya ta ce 'yan gudun hijira kimanin dubu 142 suka yi nasarar tsallakawa cikin kasar ta Italiya daga farkon wannan shekara kawo yanzu, inda amma ta ce sama da dubu uku sun halaka a kokarinsu na cimma wannan gacci.