1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-moon a ziyara a Najeriya

Ahmed Salisu/YBAugust 24, 2015

A ranar Litinin din nan ce sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce zasu ci gaba da mara baya ga Najeriya wajen ganin an samar da zaman lafiya a kasar ta hanyar ganin bayan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1GKOQ
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari und UN Generalsekretär Ban Ki-moon
Shugaba Buhari da Sakatare Ban Ki-moonHoto: DW/U. Musa

A ganawar da ya yi da mahukunta a Najeriyar Mista Ban ya jinjinawa 'yan siyasa da al'ummar kasar kan jajircewa wajen samun dorewar dimokradiyya da ma mika mulki daga tsohuwar gwamnati zuwa sabuwa ba tare da tashin hankali ba.

Mista Ban ya kuma yi wata tattaunawa da shugaban Najeriya din Muhammadu Buhari, tattaunawar da ta tabo batutuwa da dama ciki kuwa har da kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta.

Kazalika Mista Ban din ya ziyarci ofsihin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja don sanya furanni a wani mataki na girmama ma'aikatan ofishin da suka rasu sanadiyyar wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a shekarar 2011.

Nigeria - Ban Ki Moon
Bak Ki-moon da saukarsa a NajeriyaHoto: Reuters

A zantawa da manema labarai Mista Ban ya bayyana samun zaman lafiya a Najeriya a matsayin hanya da za ta kawo samun zaman lafiya a nahiyar Afirka inda ya bayyana goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wajen yaki da Boko Haram. Har-ila-yau Mr. Ban ya bayyana cewa suna goyon bayan Najeriya a fafutikar da take yi wajen ganin an kwato yaran nan 'yan makarantar Chibok da ke hannun mayakan Boko Haram.

Sakatare Ban Ki-moon ya jaddada bukatar da ke akwai wajen mutunta hakkoki na bil'Adama a yakin da kasar ta sa a gaba a yaki da Boko Haram.

Symbolbild Soldaten Nigeria
Dakarun yaki da Boko HaramHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo


A jawabinsa tun da farkon fari shugaba Buhari dama kasar sun fahimci cewar mutunta hakkin bil'adama na da muhimmanci a cikin dabarun kai karshen yakin da ta sa a gaba da BokoHaram. Kuma dole ne matakin soja su samu mutunci na dokoki na kasa da kasa kan hakkin bil'adama. Dama nazarin cewar karfin soja kadai ba zai kai karshen matsalar ba.