1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-moon ya gargadi Sudan ta Kudu

Salissou BoukariJuly 28, 2016

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna damuwarsa kan halin da ake ciki na rashin tabbas a Sudan ta Kudu tun bayan sabon rikicin da ya barke.

https://p.dw.com/p/1JXUj
UN Ban Ki Moon New York
Hoto: picture-alliance/Xinhua/Li Muzi |

Ya yin da ya ke jawabi a gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya yi kira ga hukumomin kasar da su dukufa wajen dawo da zaman lafiya a tsakanin al'umma inda ya ke cewa:

"Batun fadawa a runbun ajiya na hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da mayakan SPLA na kasar ta Sudan ta Kudu suna yi tare da sace dukannin abincin da aka tanada domin ciyar da mutane a kalla dubu 220 abu ne da ba za a laminta da shi ba kuma muna fatan wadanda suka aikata wannan danyan aiki su gurfana a gaban kuliya".

Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya, ya ce wani babban abun takaicin kuma shi ne na yadda ake samun karuwar cin zarafin mata, ta hanyar yi musu fyade, inda ya ce ma'aikatansu sun kiyasta irin wannan cin zarafi har sau 120 cikin makonni uku daga lokacin da aka samu sabon tashin hankali a birnin Juba.