1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

021013 Aufbau Ost

October 3, 2013

A daidai lokacin da Jamus ke bikin hadewa tsakanin Gabas da yammacinta, har yanzu akwai makeken gibi a fannin tattalin arziki tsakanin sassa biyu a wannan Tarayyar.

https://p.dw.com/p/19tMr
birnin Jena da ke gabashin JamusHoto: picture-alliance/dpa

Ayyukan ci-gaba guda daya bayan daya har shida shugaban gwamnatin Jamus na wannan lokaci wato Helmut Kohl, ya yi alkawarin aiwatarwa a yankin Jamus ta Gabas lokacin da sassa kasar biyu suka dunkule wuri guda. Sai dai a farko-farkon shekarun hadewarwar, Jamus ta Gabas ba ta gani a kasa ba, inda gine-gine suka ci-gaba da lalacewa, yayin da rashin aikin yi ya dada yaduwa tsakanin matasa. Lamarin da ya sa masu jin jini a jika kaura zuwa yankin Jamus ta Yamma mai karfin tattalin arziki.

Sai dai kuma shekaru 23 bayan hadin kan kasar ta Jamus al'amura sun fara inganta. Ko da shi ma Klaus-Heiner Röhl, jami'i a cibiyar nazarin tattalin arziki Jamus da ke birnin Köln, sai da ya ce sannu akan hankali kwalliya ta fara mayar da kudin sabulu a yankin gabashin Jamus.

"Wannan ci-gaban da aka shafawa al'uma mai a baka akai dai, babu yabo babu fallasa. Rashin aiki wanda a baya ya yi ma Jamus ta Gabas katutu ya ragu ainin. A fannin gine-gine ma dai akwai ci-gaba mai ma'ana da aka samu. Su ma dai kanana da kuma matsakaitan kanfanoni sun kusa kama kafafun takwarorinsu na yammacin kasa. A takaice dai an kama hanyar cimma burin da aka sa a gaba."

Klaus-Heiner Röhl, Institut der deutschen Wirtschaft Köln
Klaus-Heiner Röhl ne ya warware zare da abawa tsakanin sassa biyuHoto: IW

Banbancin marasa aiki tsakanin sassan biyu

A watan Satumban shekarar nan ta 2013 dai kashi 9,6 na 'yan Jamus ta Gabas ne suke fama da zaman kashe wando, yayin da kashi 6,6 na 'yan yankin Jamus ta yamma ke fama da rashin aiki. Lamarin da ya sha banban da shekarun baya inda yawan marasa aikin yi a yankin gabashin Jamus ya ninka na yankin takwaransa na Yamma.

A halin yanzu dau babu wasu kanfanonin da aka sansu tun fil -azan a gabashin Jamus irinsu Carl Zeiss da Jenoptik da ba da ba su bunkasa ba. Ko da manyan kanfananoni da aka san su a yankin yammacin Jamus ciki har da na kera motoci irinsu BMW da Volswagen da Daimler sun kafa rassansu a yankin gabashin kasar. Su ma dai kanfanonin da ke kera allunan samar da wutar lantarki ta haske rana ba a barsu a baya ba wajen zuba jari a Jamus ta Gabas. Amma a cewar klaus-Heiner Röhl wannan duk hangen dala ne ba shiga birni ba.

"Kama daga kanfanonin samar da wuta har i zuwa na kera motoci sun samar da guraben aiki a Yankin Jamus ta Gabas. Amma wannan ba ya na nufin cewar yankin ya kama kafar takwaransa a fannin tattalin arziki ba ne, wanda shi ne alkiblar da aka sa a gaba."

Gibin arziki tsakanin Gabas da Yamma

Wani bincike da aka gudanar ya nunar da cewa kashi biyu bisa uku na bunkasar tattalin arziki na kasashen Turai ne aka samu a yankin na gabashin Jamus. Wannan ya na nufin cewar ci-gaban yammacin Jamushar ya zarta na takwaransa na gabashin kasa da kashi daya bisa uku. Klaus-Reiner Röhl na cibiyar nazarin tatalin arzikin Jamus ya ce akwai dalili mai kwari.

Pumpspeicherwerk Goldisthal
Kanfanoni da dama na ci#gaba da zuba jari a gabashin JamusHoto: picture-alliance/ZB

"Babban banbanci da ke akwai tsakanin sassan biyu shi ne na rashin manyan kanfanoni da manyan bakuna da kuma manyan kanfanonin inshora a Gabas. Wadannan kanfafanoni ne ke daga daraja da kimar inda aka kafasu. Sai dai dukkaninsu na da cibiya ne a yankin Jamus ta yamma."

Babban abin bakin ciki ma dai a cewar Röhl shi ne matar jiya ba ta kama hanyar canza zani ba. Ya na mai cewa babu wani kwakwaran dalili da zai sa Siemens ga misali ta dauke cibiyar daga Munich ko kuma bankin Deutsche Bank ya tashi daga Frankfurt zuwa gabashin Jamus duk da banbanci albashi da ke akwai.

Mawallafi: Danhong Zhang
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe