1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangaladash: Mun kubutar da baki daga IS

Mouhamadou Awal BalarabeJuly 2, 2016

Sojojin kasar Bangaladash sun kashe 'yan bindigan IS da suka kai hari a birnin Dacca tare da kubutar da mutanen da suka yi garkuwa da su ciki har da 'yan kasashen waje.

https://p.dw.com/p/1JHra
Bangladesch Anschlag Schießerei in Dhaka
Hoto: Getty Images/M. H. Opu

Dakarun kasar Bangaladash sun yi nasarar kubutar da mutane 13 ciki har da baki uku da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a wani gidan cin abinci da ke Dacca babban birnin kasar. kakakin rundunar sojin wannan kasa Rashidul Hasan ya ce sun murkushe ilahirin 'yan bindiga 13 da suka yi mubaya ga kungiyar tsageru ta IS.

Jiya Jumma'a da maraice ne dai mutane gwammai dauke da bindigogi suka kutsa cikin gidan cin abinci na Holey Artisan bakery da ya samu karbuwa tsakanin jami'an dipolomasiya da 'yan kasashen waje, inda suka yi garkuwa da su. Dama dai kamfanin dillancin labarai na Amaq ya ruwaito cewar kungiyar IS ta dauki alhakkin wannan harin.

Wani mazuni birnin Dacca da ya shaidar da lamarin ya ce: "na ga wasu 'yan bindiga biyu da suka yi harbe-harben bindigogi. saboda haka ne na ranta a na kare. Sun rufe kofar restaurant kafin su fara kabbara a daidai lokacin da mutane ke cin abinci."