1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangui na fiskantar barazanar tsaro

Usman ShehuNovember 22, 2013

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya rikicin neman iko da kuma batun kare ɓangarorin addini na ci-gaba da dagula al'amura a ƙasar

https://p.dw.com/p/1AMFx
Young people patrol with rifles near a house destroyed by fire on October 11, 2013 in Bogangolo (171 km from Bangui). The Central African Republic, one of the poorest countries on the planet with a long history of instability, has descended into anarchy since rebels overthrew president Francoise Bozize in March 2013. Violence has surged between ex-rebels of the Seleka coalition that led the coup -- who are Muslim -- and local vigilante groups formed by Christian residents in rural areas. AFP PHOTO / PACOME PABANDJI (Photo credit should read PACOME PABANDJI/AFP/Getty Images)
Matasa dauke da makamai a BanguiHoto: PACOME PABANDJI/AFP/Getty Images

Ƙasar Faransa ta ce, mai yiwuwa wani kisan kiyashi ya faru a ƙasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Faɗa dai ya ɓarke tsakanin ƙungiyar Seleke da ke da rinjayen musulmai wanda kuma su ka karɓi ikon gwamnatin ƙasar a barar, a ɗaya gefen da kuma 'yan bindiga da ke samun goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Francois Bozize, waɗanda su ka ɗauki makamai don kare kiristoci. Ministan harkokin wajen ƙasar Faransa Laurent Fabius ya faɗa wa gidan talabijin ɗin ƙasar cewa, yanayin da ake ciki a Bangui baya kan tsari. Inda ya bayyana fatan MDD da ƙungiyar Tarayyar Afirka za su amince da shiga tsakani. An dai tura wata tawaggar kiyaye zaman lafiya a Bangui, amma bata da wani ƙarfi. A yanzu haka dai an yi kone-ƙonen Masallatai da Coci-Coci. Kiristoci dai su ne kashi 50 cikin ɗari na al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammed Abubakar