1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AfDB ya nuna damuwa kan rancen da Afirka ke karba

March 13, 2024

Shugaban Bankin Bunkasa Kasashen Afirka Akinwumi Adesina ya yi kira ga kasashen nahiyar da su kawo karshen karbar rance daga manyan kasashen duniya da ke bukatar su biya bashin da ma'adanan kasa.

https://p.dw.com/p/4dTPY
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Nedegeya

A yayin da yake magana da kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP a birnin Lagos na Najeriya, Akinwumi ya ce wannan tsari ba shi da kyau domin babu wata hanya da ake iya alkinta farashin albarkatun kasar da kasashen Afirka ke bai wa manyan kasashen na duniya wajen biyan basussukan da suka karba a irinwannan tsari.

Basussuka irin wannan ne dai ake gani suka zama dalilin karfin ikon da kasar China ta samu da wuraren hakar ma'adanai dabam-dabam na kasar Kongo, lamarin da ya kara jefa kasashen na Afirka cikin fatara.