1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baraka tsakanin 'yan tawayen Sudan ta Kudu

Abdul-raheem HassanJuly 23, 2016

Kusoshin kungiyar 'yan tawayen Sudan ta Kudu sun nada Taban Deng Gai a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa, sakamakon gudu daga Juba da Riek Machar ya yi.

https://p.dw.com/p/1JUtw
Gespräche über Waffenruhe in Südsudan Verhandlungen in Addis Abeba Taban Deng Gai
Hoto: Getachew Tedla

Wata baraka ta kunno kai a cikin tsohuwar kungiyar tawayen Sudan ta Kudu, inda kusoshinta suka nada daya daga cikinsu domin ya maye gurbin Riek Machar a matsayin mataimakin shugaban kasa. A lokacin da ya yi jawabi bayan da suka gudanar da taro a wani Otel da ke birnin Juba, Ezekiel Lol Gatkuoth ya ce sun amince Taban Deng Gai ya zama mataimakin shugaban kasa.

Shi dai Riek Machar ya gudu daga Juba babban birnin kasar, tun bayan barkewar kazamin fada da aka gwabza tsakanin dakarun shugaba Salva Kiir da na 'yan tawaye makonni biyun da suka gabata. Sai dai kafin ya arce, Machar ya sauke Taban Deng Gai da aka nada don ya gajeshi a mukaminsa na minista.