1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar Amurka a kan kasar Iran

January 19, 2005

Kasashen Turai sun bayyana rashin jin dadinsu a game da bayanan da suka fito daga bakin shugaba Bush da sakatariyarsa ta harkokin waje Condoleeza Rice dake jiran gado na cewar mai yiwuwa kasar ta tsayar da shawarar kai farmaki kan kasar Iran in har zarafi ya kama

https://p.dw.com/p/Bvdb

A lokacin da take fuskantar tambayoyi daga kwamitin kula da manufofin ketare na majalisar dattawan Amurka Condoleeza Rice tayi batu a game da tuntubar juna a maimakon wata manufa ta yin gaban kai, kamar yadda aka saba gani daga gwamnatin shugaba Bush, inda ta ce wannan lokaci ne da ya kamata a kara karfafa manufofi na diplomasiyya da kuma dinke barakar dake akwai tsakanin Amurka da wasu daga cikin kawayenta. Amma fa wannan maganar ta shafi kasashen Turai ne, banda kasashen da ba sa ga maciji da kasar ta Amurka, irinsu Iran da Koriya ta Arewa, wadanda a zamanin baya tare da kasar Irak, shugaban Amurkan George W. Bush ya kwatanta su tamkar gungun shaidanun kasashe. A halin yanzun dai hankali ya fi karkata ne zuwa ga kasar Iran dangane da ikirarin da aka yi na cewar Amurka na shirye-shiryen kai mata farmaki. Wani abin lura dangane da sakatariyar harkokin wajen Amurka mai jiran gado Condoleeza Rice, shi ne kayyadadden ra’ayin da take da shi a game da manufofin diplomasiyya da tuntubar juna, inda ta kebe kasashen Iran da Koriya ta Arewa tana mai kwatanta su tamkar makurar mulkin fir’aunanci. Kuma daidai da shugaba Bush, ita ma Condoleeza Rice ta nuna yiwuwar kai wa kasar farmaki in har zarafi ya kama. A dai kasar ta Iran a yanzun ba wanda ya yarda da bayanin da tayi daga bisani na cewar za a fara bin wata hanya ce ta laluma domin janyo hankalin kasar ta dakatar da shirinta na mallakar makaman kare dangi. Wannan maganar ma daidai take da kasashen Turai. Kasashen dai sun kasance cikin doki da murna a game da ire-iren abubuwan da suka cimma wajen tuntubar kasar Iran a diplomasiyyance, a yayinda Amurka ta gaza sakamakon matakanta na nuna karfin hatsi. Daga cikin nasarorin da kasashen na Turai suka cimma kuwa har da amincewar da Iran tayi na kin sarrafa makaman nukiliya da kuma ba wa hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa cikakkiyar damar kai ziyarar bin bahasi a tashoshinta na makamashin nukiliya akai-akai. A sakamakon haka rahotanni da bayanan da suka fito daga fadar mulki ta White House suka harzuka kasashen na Turai tare da jefa su cikin hali na rudami da rashin sanin tabbas. Domin kuwa duk wani mataki na yin gaban kanta da Amurka zata dauka ba kawai zai sake mayar da hannun agogo baya ne ga nasarorin da kasashen Jamus da Faransa da kuma Birtaniya suka cimma a shawarwarinsu da kasar Iran ba, kazalika zai kara gurbata yanayin dangantakun kasashen kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika NATO. Bayanan na Condoleeza Rice dai na bukatar gyara. Kuma ko da ta nemi fuskantar wata alkiblar din dabam ta diplomasiyya, shi shugaba Bush ga alamu bai koyi darasi daga kurakuran da ya caba dangane da Iraki ba, a sakamakon haka yake kokarin sake wani sabon yunkurin na shiga sabon rikici a wannan yanki.