1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar komawa yaki a jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya

March 18, 2013

'Yan tawayen jamhuriyar Afirlka Ta Tsakiya sun tsare ministocin kasar su biyar domin nuna adawa da gwamnatin Bozize.

https://p.dw.com/p/17zcC
Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service Soldiers from the Chadian contingent of the Central African Multinational Force (FOMAC) hold their weapons as they patrol in Damara, about 75 km (46 miles) north of Bangui January 2, 2013. Rebels in Central African Republic said they had halted their advance on the capital on Wednesday and agreed to start peace talks, averting a clash with regionally backed troops in the mineral-rich nation. REUTERS/Luc Gnago (CENTRAL AFRICAN REPUBLIC - Tags: MILITARY CIVIL UNREST POLITICS)
Hoto: Reuters

A wannan Litinin ( 18. 03. 2013), 'yan tawayen jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya sun cafke wasu ministocin kasar guda biyar, wadanda aka baiwa mukamai cikin gwamnatin hadin kan kasar da aka samar, bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da gwamnati ta kulla tare da 'yan tawayen, kana 'yan tawayen sun yi barazanar komawa fagen yaki idan har hukumomin kasar ba su biya bukatunsu ba.

Ayarin ministoci biyar din ya tafi garin Sibut ne da ke arewacin Bangui, babban birnin kasar, a matsayin wani bangare na tawagar wakilan da za su gana tare da kawancen kungiyar 'yan tawaye ta Seleka domin tattauna hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, kamar yanda ministan kula da harkokin tsaron kasar ta jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya Josue Binoua ya fadi.

Shi kuwa kanal Djouma Narkoyo na rundunar 'yan tawayen, cewa yayi suna bukatar gwamnatin shugaba Francois Bozize, ta saki daukacin fursunonin siyasa, kana da gujewa tafiyar da majalisun ministoci biyu, da kuma mutunta tanade tanaden da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma kimanin watanni biyu da suka gabata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas