1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matan Afirka da yawa ba sa amfani da wayar salula

August 13, 2019

Wayar Hannu aba ce da ta zama tamkar jamfa a Jos a wannan zamani sai dai mata da dama a nahiyar Afirka basu da ita idan aka kwatantasu da takwarorinsu maza.

https://p.dw.com/p/3NprA
Kenia Bäuerinnen erhalten per SMS Nachricht auf dem Handy
Hoto: Imago Images/photothek/T. Imo

Bisa ga wani kiyasi da aka yi kimanin mata miliyan 200 ne a nahiyar Afirka ba su kai ga mallakar wayar hannu ba a halin yanzu. Yawan matan ya sanya samun tazara ta kashi 41 cikin 100 idan aka kwatanta da mazan da ke nahiyar.

Abubuwa da dama ne dai ke hana matan mallakar waya a wannan lokaci, guda daga cikinsu kuwa shi ne matsala ta rashin ilimi kasancewar ana bukatar ilimi gwargwadon iko kafin a iya kaiwa ga amfani da waya musamman irin ta zamani wadda za a iya amfani da ita wajen shiga yanar gizo ko intanet a cewar Agnes Odhiambo wadda ke rajin kare hakkin dan Adam.

"Mutum na bukatar ya kasance mai ilimi kafin ya iya amfani da wayar hannu kana ana bukatar ilimi kafin a iya kaiwa ga shiga intanet da waya. Galibin matan da muke da su a wannan nahiya tamu na baya idan ana magana ta ilimi musamman ma idan aka dangantasu da mazan da muke da su. Wani abu har wa yau shi ne wayoyin nan fa ba arha garesu ba. Galibinsu na da tsada. Idan ka ba mace a kauye shawarar sayen waya ko kuma ta sai akuya ta kiwata ko shakka babu akuyar za ta zaba."

Wani abu har wa yau da kan sanya mata kasancewa a baya wajen mallakar waya da ma amfani da ita shi ne batun kudin da ake zubawa kafin a kai ga samun dama ta shiga intanet. Wannan ba karamin tasiri yake yi ba wajen hana mata da dama mallakar waya ko kuma amfani da ita wajen shiga intanet ga wadanda ke da wayar don sanin abin da duniya ke ciki. Irene Lourenço, 'yar asalin kasar Mozambik na daga cikin mata da dama da wannan matsala ta shafa kamar yadda ta bayyana a zantawarta da DW.

Irene Lourenço Paulino daliba daga kasar Mozambik ba ta shiga yanar gizo da wayarta
Irene Lourenço Paulino daliba daga kasar Mozambik ba ta shiga yanar gizo da wayartaHoto: DW/M. Mueia

"Ba na amfani da intanet duk kuwa da cewar ina da wayar da za a iya shiga intanet da ita. Dalilin rashin shigar kuwa shi ne tsadar da intanet ke da ita sosai wanda hakan ya sa dole na hakura. Ina son shiga sosai don samun littattafan da zan sauke don in rika karantawa amma hakan ba ya yiwuwa saboda tsadar intanet din."

Baya ga wadannan matsaloli, harkoki na al'ada ma dai na taka muhimmiyar rawa wajen hana wasu matan mallakar wayar hannu. Wasu dai na ganin abu ne da bai dace ba a ce mace ta mallaketa yayin da zafin kishi a wani bangaren kan sanya wasu mazajen mallakar waya don a tunaninsu za su iya amfani da ita su yi hulda da wadanda bai kamata a ce sun yi ba kamar yadda wata mata mai suna Aissata Fall 'yar kasar Senegal ta nunar.

Tuni dai kwararru da ma kungiyoyi da ke da ruwa da tsaki kan sabgogi na sadarwa kamar kungiyar nan ta GSMA suka fara kiraye-kirayen kawo sauyi duba da irin alfanun da hakan zai haifar ta fuskar tattalin arziki da ma cigaban matan yayin da a share guda wasu ke kiran da ilimantar da mata ta yadda zasu iya amfani da wayoyin na hannu musamman ma wanda ake shiga intanet da su don hakan zai taimaka musu ta fannoni da dama. Tuni ma dia wata kungiya ta farar hula a kasar Ghana dau gabarar zaburar da mata kan su nemi ilimi na fasahar sadarwa wanda idan da dama daga cikinsu suka samu zai taimaka wajen cike gibin da ake da shi na batun mallakar waya da mafani da ita tsakanin mata da maza a nahiyar Afirka.