1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun Euro ya mamaye taron kolin EU

October 18, 2012

Batun yadda za'a shawo kan matsalolin da kasashe masu amfani da Euro suke ciki ya dauki hankali a taron kolin kasashen 27

https://p.dw.com/p/16Sbl

Shugabannin kasashen kungiyar hadin kan Turai  wato EU, sun bude zaman taron kolinsu da shine na farko tun lokacin bazara. A lokacin taron na kwanaki biyu  a Bruessels da ake yinsa daidai lokacin da sabani ke kara tsananta tsakanin  Faransa da Jamus, za'a  maida hankali ne kan  hanyoyin farfado da tattalin arzikin nahiyar da kuma yadda  za'a kawo karshen  matsalolin kudi dake addabar kasashe masu amfani da Euro.

Shugabannin na kasashe 27 na kungiyar hadin kan Turai sun  shiga taron nasu  na kwanaki biyune a daidai lokacin da ake ci gaba fuskantar zanga-zanga a kasashe da dama masu amfani da kudin Euro, sakamakon  matakan tsuke bakin aljihu domin farfado dea tatalin arzikin su. A Girka da Spain, ma'aikata suna yajin aiki domin baiyana kara ga matakan da suka ce  sauran kawsashen masu amfani da Euro sun tilasta a kansu, abin dake kawo kuncin rayuwa da matsaloli masu yawa. Manyan kasashe biyu  dake juya akalar kungiyar ta hadin kan Turai, wato Faransa da Jamus,  suna fuskantar banbanci tsakanin su a game da  yadda za'a ci gaba da kokarin  warware matsalolin na udi da tattalin arziki. Shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel tana bukatar ganin  an ci gaba, koma an kara tsananta matakai na tsimi, musamman ga kasashe dake bukatar taimako, yayin da Faransa take son ganin an  samar da wani tsari na  hukuma daya ta hadin gwiwa da zata rika kula da  aiyukan bankuna a rukunin na kasashe masu amfani da Euro. Tun da farko sai da shugaban gwamnati ta baiyana gaban majalisar dokoki a Berlin, inda ta kare matakan da gwamnatinta take dauka a kokarin kara karfafa matsayin kudin Euro.

Tace taron kolin da aka fara yau, wanda za'a kare gobe, ba zai zama  shine na karshe ba da zai maida hankalinsa  ga kokarin shawo kan matsalolin da kudin Euro yake ciki. Za'a ci gaba da samun irin wadannan taruka, saboda kokarin karfafa matsayin Euro yana tattare ne da daukar  jerin matakai da zasu rika bin bayan juna. Tuni an sami nasarar  aiwatar da wasu matakan, inda a shekaru uku da muka shiga na fama da rikicin na kudi, mun sami nasarori masu yawa fiye da yadda muka samu a shekarun baya a Turai. Muna kuma ganin alamu na inda nasarorin namu suka nufa na kokarin  daga matsayin kudin na Euro.

Angela Merkel Bundeskanzlerin Berlin Bundestag Debatte Deutschland
Shugaban gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa

Shugaban Faransa, Francois Hollande  da tun kafin a fara taron kolin ya gana da Merkel, ya shaidawa manema labarai cewar  ya fahimci dalilan da suka sanya kasarsa da Jamus uke dabanbancin ra'ayi kan hanyoyin farfado da kudin na Euro. Yace yayin da a Faransa kwanan nan aka gudanar da zaben shugaban kasa, amma  shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel zata fuskanci masu kada kuri'u a zaben majalisar dokoki a shekara mai zuwa. Shugaban gwamnatin Austria Werner Faymann  yace lokaci yayi da za'a nunawa al'ummar nahiyar Turai cewar canje-canje suna nan tafe tattare da yadda bankuna a nahiyar suke tafiyar da aiyukasu.

Taron kolin ba zai maida hankali kan halin da Girka take ciki ba, ko da shike wata tawaga ta kasashe da kungiyoyin dake taimakawa  kasar da rancen kudi a baya-bayan nan ta kammala ziyarar gani da ido a wannan kasa.

epa03437670 (L-R)
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Francois HollandeHoto: picture-alliance/dpa

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal