1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun tsaro ne kan gaba a taron shugabannin Afirka da Obama

August 4, 2014

Shugabannin Afirka 50 ne ke ganawa a Washington don tattauna hanyoyin warware matsalar tsaro musamman saboda burin Amirka na samun damar zuba jari a kasashen nahiyar.

https://p.dw.com/p/1CobU
Barack Obama Senegal Afrika-Reise Dakar
Hoto: Reuters

Shugabannin kasashen Afirka kimanin 50 sun hallara a birnin Washington na kasar Amirka don tattaunawa da shugaba Barack Obama a kan batutuwan da suka hada da na tattalin arziki da tsaro da kuma wasu batutuwan na daban. Kasar Amirka dai na fatan samun damammakin zuba jari a nahiyar ta Afirka.

Duk da cewa birinin Washington ya saba da karbar bakwancin shugabannin da shirya taruka da toshe manyan hanyoyi. Amma a wannan Litinin kusan a ce birnin na karkashin wata dokar ta-baci, domin an rufe hanyoyin sufuri a tsakiyar birnin sannan an yi ta karkata akalar motocin safa.

Hakan ya zo ne a daidai fara taron kolin kwanaki uku na shugabannin Afirka kimanin 50 da shugaban Amirka Barack Obama ya gayyata, don cika alkawarin da ya dauka na bude sabon babin huldar dangantaku tsakanin Amirka da Afirka.

Amirka na sha'awar kara yawa jarinta a Afirka

Tun da jimawa dai kafafan yada labarun Amirkar ke mayar da hankali ga yadda kasar ke kara nuna sha'awa ga Afirka, suna masu nuni da gogayya da kamfanonin China da Indiya. Linda Thomas-Greenfield ta sashen Afirka a ma'aikatar harkokin wajen Amirka, tsohuwar jakadiyar kasar ce, cewa ta yi wannan ba shi ne farkon dangantakar Amirka da Afirka ba.

"Mun kwashe shekaru aru-aru muna hulda da Afirka. Muna da jakadu a kusan dukkan kasashen nahiyar. Saboda haka taron kolin wani karin mataki ne na karfafa dangantaka wadda da ma take da karfi."

An dai gayyaci dukkan shugabanninn Afirka nda ke da kyakkyawar hulda da Amirka. Ba a gayyaci shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ba da shugabannin kasashen Eritrea da Sudan da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A makon da ya gabata shugabannin Saliyo da Liberiya suka ce ba za su halarci gun taron ba saboda annobar cutar Ebola da ta addabi kasashensu.

Frankreich Sicherheitskonferenz in Paris Kamarun Nigeria Paul Biya und Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan da takwararsa na Kamaru Paul BiyaHoto: picture-alliance/AA

Cutar ta Ebola da kuma yaki da kungiyoyi masu kaifin kishin addini kamar Boko Haram a Najeriya na daga cikin batutuwan da za a tattauna a guna taron.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam na korafin cewa taron ya fi ba da muhimmanci ga batun ciniki ba tare da kebe isasshen lokacin tattauna yadda za a kare tsiraru ba, inji Carlos Quesada kakakin kungiyar Global Rights da ke fafatukar kare hakkin masu neman jinsi.

"Ba ni da babban fata ga taron. Shugabannin Afirka da dama 'yan mulkin kama karya ne. Akwai matsalolin keta hakkin dan Adam a wadannan kasashen. Mun san za a tattauna kan batu amma a asurce, saboda ba zai yi wani tasiri ba."

Taro babu masu rajin kare hakkin dan adam ba zai yi armashi ba

Ita ma Sarah Margon ta kungiyar Human Rights Watch ta nuna irin wannan damuwar da cewa rashin gayyatar kungiyoyin kare hakkin dan Adam zuwa taron wani babban nakasu ne.

Vorbericht USA-Afrika-Gipfel 2014
Amirka na sha'awar zuba jari a AfirkaHoto: JIM WATSON/AFP/Getty Images

To sai dai sabanin wadannan mutanen biyu, Cyrus Salabwa Kawalya dan kasar Yuganda farin cikinsa ya nuna ga taron.

" 'Yan Afirka na tasowa. Mun san yadda manufofin gwamnati ke aiki. Mu san abin da muke bukata. Saboda haka muke son mu zauna kan teburi daya mu tattauna batutuwa tsakanin da Allah."

Shi dai Cyrus Salabwa Kawalya shekaru 33 da haihuwa yana gudanar da wani aikin tallafa wa mazauna unguwanin talakawa a kasarsa, yana kuma cikin matasan Afirka 500 da aka gayyata zuwa Amirka inda suka kwashe makonni shida suna daukar karatun sanin makamar shugabanci.

Mawallafa: Simon Broll / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Pinado Abdu Waba