1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaron Nijar: Babban burin Bazoum

Gazali Abdou Tasawa LMJ
April 2, 2021

Sabon shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum wanda ya sha rantsuwar kama aiki a wannan Juma'a, ya sha alwashin hada kai da kasashe makwabta domin murkushe ayyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/3rXOH
Niger I Mohamed Bazoum
Sabon shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar Bazoum MohamedHoto: Arda Kucukkaya/AA/picture alliance

Mohamed Bazoum ya bayyan hakan ne, a cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasa a Jamhuriyar ta Nijar. Taron rantsuwar ta Bazoum dai, ya samu halartar baki daga kasashen duniya dabam-dabam. Zababben shugaban kasar dai zai tafiyar da mulki na tsawon shekaru biyar a nan gaba.

Karin Bayani: Adawa ta yi watsi da hukuncin kotu a Nijar

A jawabin nasa dai, Shugaba Mohamed Bazoum ya sha alwashin zama shugaban 'yan Nijar baki daya: "Zan zamo zababben shugaban kasa ga al'ummar Nijar baki daya. Na sha alwashin kwantar musu da hankali da hada kan 'yan kasa cikin kauna da son juna da aiki tare, domin hadin kanmu shi ne babban mataki na shawo kan kalubalen da ke addabar kasarmu na rashin tsaro da talauci. Dangane da haka ne ma, na yi wa abokin adawata Mahaman Ousmane da ma sauran shugabannin adawa tayin hawa teburin tattaunawa da su, domin samar da ingantaccen yanayin siyasa da zai taimaka ga ci-gaban kasarmu."

Mahamane Ousman Ex-Präsident Niger
Jagoran adawar Jamhuriyar Nijar Mahamane OusmaneHoto: DW/M. Kanta

Shugaba Mohamed Bazoum ya nuna damuwarsa dangane da yadda dabi'ar almundahana da yin rub da ciki da dukiyar kasa ta zamo ruwan dare a Nijar, a kan haka ne ya alkawarin nuna ba-sani ba-sabo wajen shawo kan wannan matsala. Wani batun da Shugaba Mohamed Bazoum ya ce zai kasance a sahun gaba yayin shugabancinsa shi ne na rashin tsaro da hare-haren ta'addanci da Nijar ke fuskanta: "A jihohin Diffa da Tahoua da Tillaberi, zan dauki duk matakan da suka dace domin kawo karshen azabar da al'ummomi mazaunan cikinsu ke fuskanta ta kwace da satar dabbobi da kashe-kashen ba gaira da karbar lanho da suke fuskanta daga kungiyoyin 'yan ta'adda. Zan bai wa sojojin kasarmu goyon baya 100 bisa 100, kamar yadda ta kasance lokacin mulkin Mahamadou Issoufou domin samar musu da duk kayan aikin da suke bukata wajen yaki da ayyukan ta'addanci."

Karin Bayani: Yunkurin juyin mulki a Nijar ya ci tura

Ko baya ga wakilan kasashen Turai da Amirka, bikin rantsar da sabon shugaban kasar ta Nijar ya samu halartar shugabannin Afirka guda 10 da kuma kasaitacciyar tawaga daga makobciyar kasa Najeriya. Gwamnan jihar Borno Parfesa Omara Zulum da ke zaman guda daga cikin gwamnonin Najeriya bakwai da suka halarci taron, ya bayyana fatan ci gaba da samun hadin kai da sabon shugaban wajen yakar matsalar Boko Haram. Baya ga 'yan adawa, Shugaba Bazoum ya sha alwashin inganta dangantakarsa da kungiyoyin fararen hula a Nijar, domin kawo karshen takun sakar da suka kwashe shekaru 10 suna yi da gwamnatin da ta shude.