1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bello Matawalle ya fadi a zaben gwamnan Zamfara

March 21, 2023

Hukumar zabe a jihar Zamfara ta bayyana Dauda Lawan Dare na Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben inda ya kada da gwamna mai ci na Jam'iyyar APC Bello Matawalle.

https://p.dw.com/p/4P0lO
Nigeria | Bello Matawalle
Hoto: Zaharaddeen Umar/DW

Hukumar zaben mai zaman kanta INEC ta ce dan takarar jam'iyyar PDP Dauda Lawan Dare ya samu Kur'u 377, 726 yayin da abokin hamaiyarsa Bello Matawalle na Jam'iyyar APC ya samu Kur'u  311, 976

Al'ummar jihar ta Zamfara dai na cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan sakamakon zaben.

Masana siyasa da sauran al'umma na tsokaci kan yadda Jam'iyyar adawa ta kada Gwamna mai ci a jihar ta Zamfara.

Wannan dai ba shi ne karon farko da jam'yyyar adawa da ka da gwamna mai ci ba domin hakan ya taba faruwa a kan tsohon gwamnan jihar Mamuda Aliyu Shinkafi.