1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya sanar da kudurin yin takara a 2024

April 25, 2023

Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a hukumance cewa zai sake fafata takarar ci gaba da mulkin kasar a zaben shekarar 2024, a cikin wani faifan bidiyo da ya fitar daga fadarsa ta White House.

https://p.dw.com/p/4QXzC
USA, Accokeek | Präsident Joe Biden
Hoto: Patrick Semansky/AP/picture alliance

"Yanci” wannan ita ce kalmar da Shugaba Biden ya fara fada a cikin bidiyon da ya fitar inda ya nanata jigon furicin da ya aza kamfe din zabensa na farko, watau zai cigaba da yakin tabbatar da diyaucin Amurka”, tabbatar da dorewar dimukuradiyya, ‘yanci da walwala, daidaito da mutunta juna.

Shugaba Biden bai yi magana filla-filla akan ayyukan da ya yi ba, sai dai ya roki Amurikawa da su taimaka masa ya kammala ayyukan da ya fara.

Babbar tambayar da kasar take fuskanta a shekaru masu zuwa ita ce, walau muna da karin ‘yanci da kula da hakkoki, ko kuma suna sukurkucewa?

Shugaban Amurka Joe Biden
Hoto: Leon Neal/Getty Images

Biden ya ce matsalolin a baiyane suke. A dangane da haka ne yake neman ci gaba da mulki a karo na biyu. Ya ce saboda ya san Amurka, mu mutanen kwarai ne. Ya ce na san har yanzu mu kasa ce wadda ta yadda da tsage gaskiya da mutunta kowa.

Duk da yake Shugaba Biden bai ambaci Donald Trump cikin bidiyon ba, amma ya yi shagube ta hanyar nuna harin da wasu magoya bayan Trump suka kai wa majalisar dokoki, a ranar daya ga watan Janairun shekarar 2021. Biden ya fito karara ya caccaki ‘yan MAGA, watau bangaren Republican masu tsatstsauran ra'ayi wadanda ya zarga da kokarin kassara shirin adashen gata, da kiwon lafiya, ‘yancin mata da na kada kuri'a.

Shugaban Amurka Joe Biden
Hoto: Patrick Semansky/AP Photo/picture alliance

Manyan abubuwan da za su iya taimakawa Biden a burin nasa sun hada da kokarin da ya yi wajen dakile cutar Corona, samar da karin milyoyin ayyuka, hada kan ‘yan kasa, inganta kiwon lafiya, maido da martabar Amurika a idanun kasashe dabam-dabam da kuma rage kaifin zaman zulumin da gwamnatin Trump ta jefa wasu a kasar.

Ko bayan yawancin shekaru, sauran al'amuran da za su iya zama tarnaki ga Biden sun hada da jam'iyarsa ta Demokrats, akwai mutane da yawa da ba sa son ya yi takara, saboda suna ganin ya gaji, Suna bukatar sabon jinni, sai matsalar hauhawar farashi, da makudan kudin da Amurika ta ke kashewa a yakin Ukraine. Mai yiwuwa irin wadannan matsalolin ne suka sa kwarjininsa a Amurka bai wuce kashi 40 cikin dari ba. Kazalika, duk da cewa har yanzu babu wani fitacce da zai fafata da Biden a cikin jam'iyarsa ta Demokrats, akwai yiwuwar za su sake yin fito da fito da Donald Trump, duba da cewa, duk da kararrakin da yake fuskanta, har yanzu kashi 70 cikin dari na jam'iyar Republican, suna son Trump ya sake fitowa takara a zaben shekarar 2024. Hausawa kan ce, ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.