1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin tunawa da samun 'yancin kan Najeriya

October 1, 2013

Masu fada a ji sun halarci bikin cika shekaru 53 da samun 'yancin kan Najeriya. Yayin da shi kuwa shugaba Jonathan ya yi shelar kafa kwamitin da zai sake nazarin makomar kasar .

https://p.dw.com/p/19sOK
Hoto: DW/U. Musa

Wani rukunin sojoji sun yi faretin ban girma ga shugaban tarrayar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan a bikin cikar shekarun kasar 53 da samun 'yancin kai. Sannan kuma kwarya kwaryar bikin da ya samu halarta baki dama manyan masu fada a jin cikin gwamnati ya gudana ne a bakin ofishin shugaban kasar maimakon dandalin Eagle Square da ke zaman dandanlin al'ada. Wannan dai wani abun dake nuna alamun yanayin da kasar ta samu kanta a ciki.

Matsalar tsaro na neman gagarar kundila

Kama daga zubar da jini na tashe tashen hankula ya zuwa gwargwarmayar neman iko mulkin kasar dama mummunan fatara da halin bera na shugabannin da suka ja ragamar mulkin ta cikin mafi yawan shekarun na 'yancin kai dai , kasar ta Najeriya ta wayi garin ranar tana nazarin mafita ga jerin kalubalen da suka nuna zahirin koma baya duk da ikirarin ci-gaban mahukuntan. Alamun kuma da suka kara tabbata cikin jawabin shugaban kasar na sanyin safiyar wannan talata, inda ya tabo batutuwa da dama amma kuma ya kare da biyan bukatar masu neman sake zama bisa teburi da nufin nazari na makomar kasar ta Nageriya baki daya. Shugaban kasar dai ya kammala jawabin na kusan mintuna 25 tare da sanar da wani kwamitin da zai tsara hanyoyin tattaunawar da wasu a kasar suka dade suna hankoron tabbatar da ita.

Nigeria Abuja Militärparade
Shugaba Jonathan na amfani da sojojin wajen warware matsalar tsaro a arewacin NajeriyaHoto: DW/U. Musa

In akwai batutuwa dake daga hankali dama neman jawo matsala, ya zama babbar dabara ga wadanda abun ya shafa su zauna don tattaunawa. Don tabbatar da imani bisa karfin tattaunawa wajen warware matsaloli, na yanke hukuncin kafa wani kwamitin ba da shawara domin tsara hanyoyin gudanar da tattaunawa ko kuma taro na kasa.”

Muhara kan kwamitin bada da shawara

Duk da cewar dai babu rana balle wuri na fara tattaunawar, tuni matsayin na gwamanti ya fara jawo muhawara a bangarorin da suka taka rawa na lokaci mai tsawo wajen kai Najriyar ya zuwa inda take a yanzu haka. Farfesa Jerry Gana dai na zaman jigo a jam'iyyar PDP kuma mai fafutuka na kananan kabilun arewacin tarrayar Najeriyar, kuma a fadarsa lale marhabin da sabon tayin na gwamnatin kasar ya yi. Tun da farkon fari dama shugaban majalisar dattawan kasar David Mark ya ce yana goyon baya ga shirya taron da masu son tsarashi ke tunani na sauyin rawa game da kudin shiga dama tsarin mulkin da kasar ke tafiya kai.

To sai dai kuma a cewar General Oladipo Diya mai ritaya da a baya ke zaman mataimakin shugaban kasa a gwamnatin marigayi Abacha, matsalar kasar ta Najeriya ba matsala ta rashin kiran taruka bane.

29.09.2013 DW online Karte Karussel Nigeria Abuja Yobe Gujba
Yobe na cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

"ko a lokacin zamaninmu mun kira taron da ya amince da amfani da kundin tsarin mulki na shekara ta 1979 amma jim kadan bayan nan halin al'ada ya fito. Bukatarmu ina jin ita ce ta sauyin hallaya. In da kira aka yi na taron sauya hali kamun taro na kasa da kila ya fi zama hanyar fita a garemu."

An dai gudanar da taron na fadar shugaban kasar ne tare da kauracewar akalla hudu cikin shida na ragowar shugabannin da suka ja ragamar mulkin kasar na shekarun 53.

Mawallafi: Ubale Musa daga Abuja
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe