1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike kan dukiyar tsohon shugaban Gabon

Gazali Abdou/MAApril 9, 2015

Ana can ana ta tabka muhawara a kasar Gabon tsakanin gwamnati mai mulki da jam'iyyun adawa kan dukiyar da tsohon shugaban kasar da wasu na kusa da shi suka mallaka.

https://p.dw.com/p/1F5aY
Hoto: AP

A ranar Alhamis ce dai kawancen jam'iyyun adawar kasar ta Gabon su ka shirya wani babban gangami a birnin Libreville domin neman a gudanar da bincike a kan dukiyar iyalan tsohon shugaban da su ke zargi da wawure dukiyar kasar.

Watanni da dama kenan da wannan babban kawance wanda ya kunshi yan siyasa da kungiyoyi masu rajin canji a kasar, mai suna Front Uni de l´opposition pour l,alternance ya ke ta faman fadi tashi da nazarin duk hanyoyin da su ka dace domin kwatowa kasar kudadenta da su ka ce suna zargin iyalan tsohon shugaban wato Omar Bango sun yi rub da ciki a kansu.

Gabun Wahlen 2009 Wähler in Libreville
Taron jama'a kan binciken dukiyar tsohon shugaban kasar GabonHoto: AP

Jean Didier Moukangni Uwangou da ke zaman jagoran kawancan 'yan adawa a kasar ya ce ''kungiyarmu na bukatar ganin an bi hanyoyin doka domin sanin hakikanin gado da tsohon shugaban ya barwa iyalinsa da kuma sanin adadin kadara da dukiyar da ya bari sannan muna bukatar a tantance abinda ya ke halalin iyalan nasa da abinda ya kamata koma mallakin kasa.''

Wani batun na daban da ke zama babbar mahawara a yanzu a kasar ta Gabon shi ne ta neman tantance a zahiri su wa za a kira magadan tsohon shugaban kasar. Sai dai 'yan adawar sun dage taron da suka tsara har zuwa ranar Asabar saboda tsaiko da aka samu daga jami'an tsaro.