1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken jirgin AirAsia a rana ta uku

December 30, 2014

An dai fara gano wasu komatsai da ake zaton daga jirgin ne bayan da tun farko aka ce an ga hayaki na tashi a tekun na Java sai dai wasu masanan na cewa babu tabbaci.

https://p.dw.com/p/1ECEg
AirAsia Airbus 320-200 vermisst 30.12.2014
Hoto: ADEK BERRY/AFP/Getty Images

An shiga rana ta uku cikin aikin binciken jirgin Indonesiya na AirAsia da ya yi batan dabo a karshen makon daya gabata. A na dai kyautata zaton jirgin mai lamba 8501 ya fada ne cikin tekun Java.

Akwai dai rahotanni da ke cewa an ga hayaki na tashi a wani sashi na tekun a yayin da ake fadada wannan aikin bincike. Sannan wasu rahotannin yanzu na nuna cewa an ga wasu sassa da ake zaton na jirgin ne a tekun na Java.

Da yawa dai masana na ganin cewa jirgin ta yiwu a gano shi karkashin teku kasancewar yana saman tekun lokacin da aka rasa samun bayanansa.

Wannan dai jirgi na AirAsia na kan hanyarsa ne daga Indonesiya zuwa kasar Singapore dauke da fasinjoji 162 mafi yawansu daga kasar ta Indonesiya.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu