1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken tauraruwa mai wutsiya na kasashen Turai ya kankama

November 12, 2014

Irin wannan bincike a shekarun baya na gamuwa da cikas amma a wannan karo masana kimiyar samaniya na ganin alamun sauya tunani a duniyar binciken samaniya.

https://p.dw.com/p/1Dm5K
Raumfahrt ESA Weltraumsonde Rosetta - Tschurjumow-Gerassimenko Komet
Hoto: Reuters/ESA/Rosetta/NAVCAM/CC BY-SA IGO 3.0

Bayan kwashe miliyoyin mila-milai daga wannan duniya tamu yana tafiya a sararin samaniya kumbon binciken kasashen Turai ya saki mutummumin da zai yi bincike a tauraruwa me wutsiya Comet a Turance ta yadda za a rika samar da bayanai da za su hada da lalubo yadda duniya ta samo asali.

Paolo Ferri, shi ne jagoran wannan shirin binciken samaniya a Jamus:

Ya ce "Mun riga mun samar da banbanci kuma mun kafa tarihi da nasara".

Masu binciken a cibiyar samaniya Darmstadt a Jamus na samun bayanan saukar wannan mutum mutumi sun shiga murna.

To ko wannan nasara me take nufi a duniyar binciken kimiyar samaniya? Farfesa Yusuf Adamu masani ne na kimiyar muhallin dan 'Adam a jami'ar Bayero da ke Kano a Najeriya:

"Wannan na iya sauya tunanin mu kan asalin yadda duniya ta samo asali."

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo