1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta amince da kawance 'yan adawan Siriya

November 21, 2012

Majalisar gudanarwar 'yan adawan Siriya na ci gaba da samun goyon baya, inda Birtaniya ta shiga cikin wadanda su ka amince da ita.

https://p.dw.com/p/16n4g
Hoto: AFP/Getty Images

Ƙasar Birtaniya ta amince da sabuwar majalisar 'yan adawan ƙasar Siriya, a matsayin mai wakiltar al'umar ƙasar, wannan yayin da babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon, ya nuna damuwa kan yadda ƙasar ke neman zama fagen yaƙin na yankin.

'Yan tawayen na ci gaba da samun goyon baya na diplomasiya, inda Birtaniyar ta zama kasa ta tara da ta amince da su, bayan kasashen Faransa, Turkiya da kuma kasashen Larabawa na yankin tekun Gulf.

Haka na zuwa yayin da rahotanni ke cewa dakarun gwamnatin ƙasar ta Siriya sun fatattaki 'yan tawayen cikin tungar su da ke wajen Damascus babban birnin ƙasar. Shugaban Bashar al-Assad na ci gaba da matsin lamba bisa wannan rikici da ke laƙume rayuka.

Mawallafi: Suleiman Babayo

Edita: Mohammad Nasir Awal