1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta kai hari a jihar Yobe

Al-Amin Muhammad/ MABMay 31, 2015

'Yan bindiga sun kona gidaje da shaguna a wasu garuruwa na jihar Yobe na tarayyar Najeriya

https://p.dw.com/p/1FZjC
Hoto: Reuters/Emmanuel Braun

Wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan Kungiyar Boko Haram ne sun kai wasu jerin hare-haren a daren jiya Asabar a garuruwan Fika da Ngalda a jihar Yobe da ke tarayyar Najeriya, inda suka kona gidaje na jama’a da ma’aikatun gwamnati da kuma cibiyoyin sadarwa. Al’ummar garuruwan da ke makwabtaka da su sun bayyana cewa sun kwashe daren jiya suna jin karajin harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa da ake zaton Bama-Bamai ne.

‘Yan bindigar wadanda ake zaton sun fito ne daga daji a jihar Yobe sun fara kai harin a garin Ngalda wanda ke kan iyakar jihohin Gombe da Yobe, inda suka fasa shaguna, suka kuma yi awon gaba da kayayyaki da dama. Daga nan suka je garin Anzai da Fika inda suka kona Sakatariya da Ofishin ‘yan Sanda da wasu gidajen Jama’a mallakar gwamnati.

Ya zuwa yanzu dai babu alkaluma na yawan wadanda suka mutu ko kuma suka jikata a wadannan hare-hare na Yobe.